Hausa Times NG

Hausa Times NG Hausa Times NG tashayar yaɗa labarai ce, dake yaɗa ayyukan ta a kafafen sada zumunta, wacce zatana kawo muku sahihin labarai cikin harshen Hausa.

"Ba za mu bari kowa ya zalunce mu ba, ko ya haɗa baki da wasu domin cutar da mu ko tauye haƙƙin mutanenmu a Doguwa da Tu...
17/02/2026

"Ba za mu bari kowa ya zalunce mu ba, ko ya haɗa baki da wasu domin cutar da mu ko tauye haƙƙin mutanenmu a Doguwa da Tudun Wada".

"Idan akwai wani yanki kai tsaye na jam’iyyar APC a Jihar Kano, to Doguwa da Tudun Wada ne. Saboda haka babu dalilin da zai sa wani munafuki, komai girmansa, ya je ya haɗa baki da wasu domin hana mu haƙƙin ƙaramar hukumar Tudun Wada a hannun ’yan asalin jam’iyyar APC".

"Za mu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da Mai Girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin da ya yi wa kowa na zama shugaba mai adalci. Kuma tabbas Mai Girma Gwamna zai same mu masu aminci tare da tabbatar da nasararsa a zaɓe mai zuwa, Insha Allah", in ji Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya jagoranci wata tawaga zuwa Kano domin jajantawa kan gobarar da ta janyo...
17/02/2026

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya jagoranci wata tawaga zuwa Kano domin jajantawa kan gobarar da ta janyo ɗimbin asarar dukiya a kasuwar Singer.

A ranar ta Litinin kuma Shettima ya karɓi Gwamna Abba Kabir a jamʼiyyar ta APC a hukumance yayin ziyarar.

Kano ta kuma samu tallafin ƙarin Naira biliyan uku daga wasu gwamnoni, hakan ya sa tallafin ya zama Naira biliyan takwas.

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu wani batu a hukumance da aka gabatar a gabanta dangane da shirin sauke mataimaki...
31/01/2026

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu wani batu a hukumance da aka gabatar a gabanta dangane da shirin sauke mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo.

Mai magana da yawun majalisar, Kamal Shawai ne bayyana hakan yayin tattaunawa da Premier Radio 102.7 FM.

Kamal Shawai ya karyata labarin da ake yadawa cewa majalisar ta baiwa mataimakin gwamnan Aminu Abdussalam Gwarzo wa'adin kwanki biyu ya sauka daga kujerarsa.

A cewarsa yanzu haka majalisar tana hutu, kuma sai cikin watan Fabrairu majalisar za ta dawo daga hutu.

Wani harin mayakan Boko Haram s**a kan masu aikin gyran gada a ƙauyen Wajiruko na ƙaramar hukumar Damboa a jihar Barno y...
31/01/2026

Wani harin mayakan Boko Haram s**a kan masu aikin gyran gada a ƙauyen Wajiruko na ƙaramar hukumar Damboa a jihar Barno ya yi sanaɗin mutuwar mutane da dama ciki har da sojoji da jami'an sakai na JTF da kuma fararen hula.

Rikicin Masarautar Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Sanusi II zai ci gaba da zama Sarki babu batun sauyi.Biyo bayan d...
31/01/2026

Rikicin Masarautar Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Sanusi II zai ci gaba da zama Sarki babu batun sauyi.

Biyo bayan daidaituwar siyasar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da gwamnatin tarayya, an sake samun ce-ce-ku-ce a faɗin jihar Kano kan makomar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, musamman dangane da tsohon rikicin masarautar Kano da bai gama lafa ba.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito karara ya karyata jita-jitar da ke cewa sauyin siyasar nasa na iya shafar matsayin Muhammadu Sanusi II. Gwamnan ya jaddada cewa babu wani shiri na sauya ko cire Sanusi II daga sarautar Kano, yana mai cewa komai an yi shi ne bisa doka da ka’ida

Iran ta sanar da cewa za ta fara atisayen sojan ruwa (live-fire drills) a kusa da Strait of Hormuz da Tekun Oman, inda m...
31/01/2026

Iran ta sanar da cewa za ta fara atisayen sojan ruwa (live-fire drills) a kusa da Strait of Hormuz da Tekun Oman, inda manyan jiragen yakin Amurka ka ke kusa da wurin a yankin. Atisayen, wanda zai ɗauki kwanaki, ya zo ne a lokacin da tashin hankali tsakanin Iran da Amurka ke ƙaruwa. Amurka ta yi gargadi cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya zama haɗari ko tayar da rikici ba. Masana na ganin cewa duk wani rikici a Strait of Hormuz na iya shafar zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwar man fetur ta duniya, domin muhimmancin yankin wajen fitar da mai.

Shin ko kuna ganin Murtala Sule Garo ya dace da ya zama mataimakin gwamnan jahar Kano, idan Kwamared Aminu Abdulsalam ya...
29/01/2026

Shin ko kuna ganin Murtala Sule Garo ya dace da ya zama mataimakin gwamnan jahar Kano, idan Kwamared Aminu Abdulsalam yayi murabus?

A wani bangare na kokarin bunkasa wasanni da kuma hadin gwiwar matasa a Zamfara ,Gwamnan Dauda Lawal Dare ya karbi bakun...
29/01/2026

A wani bangare na kokarin bunkasa wasanni da kuma hadin gwiwar matasa a Zamfara ,Gwamnan Dauda Lawal Dare ya karbi bakuncin babban Kocin Super Eagles, Éric Sékou Chelle, a fadar gwamnati da ke Gusau,

Faransa za ta goyi bayan matakin da Italiya ta jagoranta domin Tarayyar Turai EU ta ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Ha...
29/01/2026

Faransa za ta goyi bayan matakin da Italiya ta jagoranta domin Tarayyar Turai EU ta ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addanci, sakamakon zarginta da kisan ɗaruruwan masu zanga zangar kin jinin gwamnati, kamar yadda Fadar gwamnati ta Élysée ta sanar.

NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya yi murabus
29/01/2026

NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya yi murabus

Babban Mataimakin Mai Tsara Rundunar Sojin Iran: Ya bayyana cewa, Idan Amurka da Isra'ila suyi Gangancin kai hari Iran, ...
29/01/2026

Babban Mataimakin Mai Tsara Rundunar Sojin Iran: Ya bayyana cewa, Idan Amurka da Isra'ila suyi Gangancin kai hari Iran, martanin sojojin mu zai zama na ban mamaki. Wanda zai jawo musu mummunar Asara.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gagarumin bikin tarbar Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a Ankara.A ranar...
27/01/2026

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gagarumin bikin tarbar Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a Ankara.
A ranar Talata ne aka yi wa Shugaba Tinubu fareti na musamman don girmamawa.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Times NG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share