Nigerian Hausa News

Nigerian Hausa News Nigerian Hausa News sabuwar jarida ce ta yanar gizo wacce zatana kawo muku sahihin labarai cikin harshen Hausa da Turanci

16/4/2021. 4/Ramadan/1442

Kwastam ta k**a buhuna shinkafa 250 da aka boye a cikin tankar mai a KadunaHakanan, rundunar ta mika wasu magunguna da k...
06/08/2025

Kwastam ta k**a buhuna shinkafa 250 da aka boye a cikin tankar mai a Kaduna

Hakanan, rundunar ta mika wasu magunguna da kayayyakin sinadarai masu hadari da ta k**a ga Hukumar NAFDAC da NESREA domin daukar mataki.

Time to Face the Truth"Ladies and gentlemen,Today, I want us to ask ourselves one bold question: Who is truly to blame f...
06/08/2025

Time to Face the Truth"

Ladies and gentlemen,

Today, I want us to ask ourselves one bold question: Who is truly to blame for the underdevelopment of Northern Nigeria?

We have seen the decline, in education, healthcare, infrastructure, and security. And yet, this region has produced powerful governors, senators, ministers, even presidents. So, what happened?

Let us remember the legacy of Sir Ahmadu Bello, the Sardauna of Sokoto. He built schools, invested in agriculture, and united our people. He had a vision — one where the North would rise in dignity, strength, and self-reliance.

But can we say the same for today’s leaders?

Instead of progress, what we see is blame! blaming the South, blaming the West, blaming history. But the truth is clear: the North is being held down by its own leaders, those who were entrusted with the future but chose personal wealth and power instead.

Our children are on the streets with bowls, not books. Our hospitals are collapsing. Our youth are unemployed and angry. And yet, we have billionaires, powerful politicians, and influential clerics,all silent when it matters most.

It is time to stop the excuses. The North must wake up. We need leaders who will rise with courage, sacrifice, and love for their people. Leaders who will invest in education, empower women, and heal our communities.

Because until then, Northern Nigeria will remain a sleeping giant — chained, not by outsiders, but by its own gatekeepers.

Zainab Bello (DWLN)
Director Media and publicity Nigeria First

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, ci gaban al’umma,...
03/07/2025

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, ci gaban al’umma, da kuma haɗa kowa da kowa cikin ci gaban ƙasa ta hanyar gina muhimman ayyuka. Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba wai kawai tana gina tituna ba ne, amma tana shimfiɗa hanyoyin nasara mai dorewa, da kuma damar samun ci gaba, da walwala ga ‘yan Najeriya.

Amarya da uwar gida tun a waje normal suke sun Saba ba ruwansu ga ango a gefe suna baza capacity Allah yabasu zaman lafi...
26/04/2025

Amarya da uwar gida tun a waje normal suke sun Saba ba ruwansu ga ango a gefe suna baza capacity Allah yabasu zaman lafiya👌🏻💯🌹

15/04/2025

Manyan manoman arewacin Najeriya sun fara komawa kudancin ƙasar, inda suke samun tsaro da kwanciyar hankali.
Tuni ɗaya daga cikin ƴan arewar ya mallaki gonar shinkafa mafi girma a kudancin Najeriyar.

Tarayyar Turai za ta tallafa wa gwamnatin Falasɗinawa da dala biliyan 1.8
15/04/2025

Tarayyar Turai za ta tallafa wa gwamnatin Falasɗinawa da dala biliyan 1.8

An samu tashin gobara a Kasuwar Kafintoci da ke Gandun Albasa a Kano.📸 Abdulhamid Abdullahi Aliyu
07/04/2025

An samu tashin gobara a Kasuwar Kafintoci da ke Gandun Albasa a Kano.

📸 Abdulhamid Abdullahi Aliyu

A halin yanzu, dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da China tana cikin rikici mai tsanani. A ranar 7 ga Afrilu, 2025, ...
07/04/2025

A halin yanzu, dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da China tana cikin rikici mai tsanani. A ranar 7 ga Afrilu, 2025, tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙara haraji na kashi 50% kan kayan da ake shigo da su daga China, muddin China ba ta janye ƙarin harajin kashi 34% da ta kakabawa kayan Amurka ba. Wannan ƙarin haraji na China ya kasance martani ne ga harajin kashi 34% da Trump ya fara kakabawa kayan China a baya. Trump ya ba China wa'adin zuwa 8 ga Afrilu don janye wannan haraji, in ba haka ba, za a fara aiwatar da sabon harajin kashi 50% daga 9 ga Afrilu. Bugu da kari, Trump ya bayyana cewa duk wata tattaunawa da China za a dakatar da ita idan ba a warware batun ba. Wannan matakin ya haifar da fargaba a kasuwannin duniya, inda masu saka jari ke nuna damuwa game da yiwuwar durkushewar tattalin arziki.

A nasa bangaren, China ta mayar da martani ta hanyar ƙara haraji na kashi 34% kan duk kayan da ake shigo da su daga Amurka, wanda za a fara aiwatarwa daga 10 ga Afrilu, 2025. Haka kuma, China ta sanya takunkumi kan fitar da wasu kayayyaki masu mahimmanci k**ar wasu nau'in ma'adanai, tare da ƙara wasu kamfanonin Amurka guda 11 cikin jerin "ɓatattun ƙungiyoyi". Wannan matakin ya nuna cewa China tana ɗaukar tsauraran matakai don kare muradunta a fannin kasuwanci.

Wannan rikicin kasuwanci yana da babbar illa ga tattalin arzikin duniya, tare da haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rage yawan kayan da ake fitarwa da shigo da su tsakanin ƙasashen biyu. Masu nazari suna nuna damuwa cewa wannan rikicin na iya jefa duniya cikin matsin tattalin arziki, musamman ma idan aka ci gaba da ɗaukar matakan ramuwar gayya tsakanin Amurka da China.

A takaice, halin da ake ciki yanzu tsakanin Amurka da China a fannin haraji yana nuna ƙaruwar rikici da rashin fahimta, wanda ke haifar da damuwa a kasuwannin duniya da kuma tattalin arzikin ƙasashen biyu.

Kai Tsaye Daga Wajen Jana’izar Alhaji Abbas Sununu Galadiman Kano Da Allah Ya Yiwa Rasuwa Jiya Talata.
02/04/2025

Kai Tsaye Daga Wajen Jana’izar Alhaji Abbas Sununu Galadiman Kano Da Allah Ya Yiwa Rasuwa Jiya Talata.

Wata majiy.Jami'an tsaro sun budewa 'yan shi'a wuta a Abuja.
28/03/2025

Wata majiy.

Jami'an tsaro sun budewa 'yan shi'a wuta a Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandar jahar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa  ya sanar da cewa babu hawan Sallar a jahar Kano.Shin me...
28/03/2025

Kakakin rundunar 'yan sandar jahar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da cewa babu hawan Sallar a jahar Kano.

Shin me zaku ce?

Wani bidiyo dake yawo yadda aka  kona wasu farauta Hausa/Fulani  'yan Arewacin Nigeria , mafarautan sun fito daga Porta ...
28/03/2025

Wani bidiyo dake yawo yadda aka kona wasu farauta Hausa/Fulani 'yan Arewacin Nigeria , mafarautan sun fito daga Porta Court zuwa Kano, sun kawo wani gari dake ce.masa Uromi a jahar Edo, a nan 'yan garin s**ace 'yan kidnapping ne, a nan s**a banka musu wuta.

Mun samu rahoto daga Ahmed B Muhammad wanda abin ya faru a gabansa.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigerian Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share