09/06/2025
An Bukaci Shugaban NAHCON Ya Yi Sujudad Shukr Ga Allah Kan Nasarar Da Aka Cimma Wajen Hada-hadar Masha'ir Na Hajjin 2025
Duk da kalubale masu tarin yawa da s**a hada da kamfen din batanci da aka shirya domin bata sunan shugabanci, da kuma koke-koke da korafe-korafe da dama da aka shigar a kansa, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Usman ta yi abin al’ajabi, inda ta gudanar da daya daga cikin mafi nasara wajen shirya ayyukan Masha’ir (wurin gudanar da manyan ibadu na Hajj) a cikin tarihin hajjin baya-bayan nan.
Masu ruwa da tsaki da kuma mahajjata na ci gaba da yaba wa hukumar bisa yadda ta gudanar da aiki cikin tsari daga harkokin sufuri, walwala, da kuma jin dadin mahajjata, musamman a ranakun kololuwa na Hajj a Mina, Arafat da Muzdalifa. Wasu daga cikin jama’a sun bukaci Farfesa Abdullahi Saleh Usman tare da tawagarsa da su gudanar da sujudad shukr wato su durkusawa cikin sujada don nuna godiya ga Allah saboda irin wannan babbar nasara da aka samu duk da wahalhalun da aka fuskanta kafin nan.
Tun daga farko, shugabancin yanzu ya fuskanci tsangwama daga wasu bangarori da ke kokarin bata masa suna ta kafafen watsa labarai, tare da shigar da korafe-korafe marasa tushe domin dakile sauye-sauyen da Farfesa Abdullahi ya kuduri aniyar aiwatarwa. Wadannan hare-hare sun bar hukumar cikin wani hali na kunci da kuma kalubalen gina sahihanci da karfin guiwa.
Sai dai da jajircewa, gaskiya, da kuma sabuwar manufa ta kyautata wa mahajjatan Najeriya, shugabancin NAHCON ya ci gaba da yin abin a zo a gani, inda aikin da s**a yi ya yi magana da kansa.
Rahotanni daga kasa mai tsarki sun tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya sun samu kyakkyawan sufuri, ingantaccen abinci, da tsare-tsaren tent da s**a fi na baya tsafta da gyara, tare da ingantattun ayyukan lafiya a Masha’ir. Da dama daga cikin mahajjatan sun bayyana gamsuwarsu, wasu ma suna cewa wannan shekarar ita ce mafi kyau cikin shekaru goma da s**a gabata.
Alhaji Sani Muhammad Hotoro, daya daga cikin mahajjatan daga jihar Kano, ya ce: “Dole ne mu gode wa Allah sannan mu gode wa shugabannin NAHCON. Mun karanta labaran batanci kafin Hajj, amma abin da muka gani a nan wani abu ne dabam. Komai ya tafi daidai daga Mina zuwa Arafat har zuwa Muzdalifa. Muna alfahari da hukumar mu.”
Hajiya Fatima Ibrahim daga jihar Legas ta kara da cewa: “Ni na je Hajj sau shida, amma wannan shekarar ita ce mafi inganci wajen shirya Masha’ir. Allah ya saka wa hukumar NAHCON da alheri, kuma ya ci gaba da jagorantar su.”
Lallai, irin yadda aka gudanar da Masha’ir cikin nasara da lumana wannan shekarar ya nuna kwarewar hukumar NAHCON wajen tsara abubuwa, hadin guiwa da hukumomin Saudiyya, tare da taimakon Allah mai girma. Ba abin mamaki ba ne da mutane ke bukatar shugaban NAHCON da tawagarsa da su gudanar da sujudad shukr saboda Allah ya sauya wahala zuwa nasara.
Yayin da hajjin shekarar 2025 ke gab da karewa, abu daya ya tabbata: Farfesa Abdullahi Saleh Usman da tawagarsa sun cancanci yabo, sun kuma kafa sabon misali da sauran shugabanni za su iya dora a kai wajen gudanar da hajji a nan gaba.