14/01/2024
Hakika an yiwa dimokradiya mahangurba, kuma an wulakantar da mutunci, kwarjini da karfin iKon judiciary a kasar nan.
Alkalai da kotuna sune dama ta karshe da mai hakki ko Wanda aka zalunta suke da ita domin Kai kokensu bisa tsammanin samun adalci. Amma Kash, a yau alkalai da duk wani tsari na shari'a an karya shi, martaba da tasirin alkalai ya fadi kasa warwas.
Hukuncin karshe na Shari'ar Kano babban misali ne ga mawuyacin halin da demokradiya ta fada ciki, tare da tauye duk wani yanci da kotunoni ko alkalai suke dashi don wanzuwar adalci.
Hukuncin Shari'ar Kano a yau cikakken misali ne da ke nuna gurbacewar al'amuran siyasa a kasar nan musamman ta fuskoki guda biyu:-
1. An budewa Jam'iyun siyasa a nan gaba kofar yin magudi da chusa kuri'un bogi a lokutan zabe,domin Koda anje kotu zasu iya tsira.
2. An tauye hakki da yancin masu zabe, domin anan gaba ma mutane zasu Dena wahalar da kansu fita yin zabe. Domin suna zabar abinda sukeso, wasu suna aringizo da chushen kuri'a ana basu.
3. A nan gaba mutane bazasu dinga damuwa da cika duk wasu ka'idoji na tsayawa takara ba, domin kuwa kotu da alkalai a hukuncin kotun koli sun tabbatar da hakan. Kuma sun yiwa duk wata dokar zabe Karan tsaye, Wanda hakan dabawa kansu wuka ne sukayi domin anan gaba basu Isa suyi hukunci da ya sabawa wannan ba. Suma zasu kuka da kansu.
4. Ba'ayi adalci ba a hukuncin Kano, domin kuwa mao sharia Babu wata doka ko reference da ya dogara dasu wajen yanke hukuncin Kano, kawai ya karanto bayanansa a matsayin raayi, kamar yadda ya bayyana kuma yayi mana hukunci da raayinsa duk da cewa alkali ne, Amma ya maida Kansa baya, ya yarda ya nuna.rashin kwarewa, ya lalata image na sharia saboda son zuciyarsu.
Daga karshe zamu zo da bayanai masu yawa kan duk wasu kulle kulle da akayi akan wannan sharia Wanda har yasa AKAI wannan danyen hukuncin.
yin hakan bazai haifar da kowace irin matsala ba domin Koda kotu akaje barawon kuri'u zai iya tsira de
tabbatar da irin halin innanillahi wa Inna ilaihir raji'un da aka samu Kai a ciki ta fuskar abubuwa guda biyu