12/07/2026
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
A safiyar ranar da aka shirya ɗaura aurensa, ta zamo aka yi jana'izarsa.
Marigayi Muhammad Kabir Danjuma ya shafe shekaru masu yawa yana neman ilimi tare da gina makomarsa. Sedai kuma a ranar da Iyalai, abokai da masoyansa s**a kammala duk shirye-shiryen bikin aurensa, amma ƙaddarar Allah ta riga fata.
A daidai ranar da aka tanada domin ya fara sabuwar rayuwa tare da amaryarsa, ita ce ta zama ranar da aka yi masa bankwana zuwa makwancinsa na ƙarshe.
Lallai wannan al'amari babban darasi ne ga kowa. Rayuwa ba ta da tabbas, kuma babu wanda ya san lokacin da ajalinsa zai cika. Saboda haka, mu yawaita aikata alheri, mu kyautata alaƙarmu da Allah da kuma mutane, domin mutuwa ba ta sanarwa.
Allah Ya jiƙan Muhammad Kabir Danjuma, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba iyalansa, amaryarsa da dukkan masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.
Allah Ya jiƙansa da rahama. 🤲🙏🏻🙏🏻🙏🏻