29/09/2025
ALHAMDULILLAH GSKY WANNAN ABUN A YABA NE
Matsashin ɗan Crypto daga Arewacin Najeriya mai suna Sunusi Danjuma Ali ya wayi gari ya ga kuɗi sama da $135,000 (fiye da Naira miliyan 200) a asusunsa na Bitunix cryptocurrency.
A cewar Sunusi, ya yanke shawarar sanar da kamfanin tare da mayar da kuɗin gaba ɗaya, abin da ya jawo masa yabo da taya murna daga mutane da dama a shafukan sada zumunta.
Muna fatan wannan matakin nasa daya dauka yazama abin koyi ga matasa da al’umma baki ɗaya kan muhimmancin gaskiya da amana a harkokin kuɗi na zamani.
Wane fata za Ku yiwa Sunusi?