Digital Muktar

Digital Muktar Do not do anything from which you will not gain either money or reward by allah.
(1)

Update 🇨🇳✨ china zata gabatar da Sabuwar  Visa Daga ranar 1 ga Oktoba 2025, kasar China za ta kaddamar da sabon K-Visa d...
24/09/2025

Update

🇨🇳✨ china zata gabatar da Sabuwar Visa

Daga ranar 1 ga Oktoba 2025, kasar China za ta kaddamar da sabon K-Visa domin jawo ƙwararrun matasa a fannin kimiyya da fasaha daga ko’ina cikin duniya.

🔹 K-Visa bata buƙatar sai akwai mai ɗaukar nauyin ka kafin kashiga kasar Kamar ta Amerika.
🔹 kuma zata baka damar shiga kasar sau dayawa ba Kamar ta Amerika ba.
🔹 sannan zaka iya amfani da visar wajen shiga bincike na kimiyya, musayar al’adu, har ma da kasuwanci.

Wannan shirin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ta ɗora harajin $100,000 kan H-1B visa — wanda ya fi shafar ma’aikata daga Indiya (71%) da China (11.7%).

👉 chaina da a yanzu za iya cewa zata iya zama cibiyar fasaha ta duniya nan da shekarar 2035

Technology Update🇩🇪☀️ Injiniyoyin a kasar Jamus sun ƙirƙiri sabuwar solar panel (Transparency ) mai gilashi!Wannan fasah...
24/09/2025

Technology Update

🇩🇪☀️ Injiniyoyin a kasar Jamus sun ƙirƙiri sabuwar solar panel (Transparency ) mai gilashi!

Wannan fasaha ana sata tayi aiki a matsayin tagar daki,yanda haske na shiguwa ita kuma na Samar da wutar lantarki.

🔹wanda Ake amfani da kayan organic photovoltaic waɗanda idon ɗan Adam yana iya ganin haske ta cikin su, amma suna mai da ultraviolet da infrared zuwa lantarki.

🔹 Wannan na nufin tagogin gida, ofisoshi ko manyan gina-gine za su iya amfani dashi wajen cajin waya da fitilu don rage dogaro da wutar gwamnati.

Wanda ana ganin nan gaba, manyan gine-gine na gilashi gaba ɗaya za su iya zama matattarar samar da wuta a cikin birane! 🌍⚡

👉 Ku fada mana ra'ayinku a comment section.



Digital Muktar

Tech Update;🎓 Google Ta Yi lunch din AI Free Courses tare da Certificates 2026Google ta ƙaddamar da sabbin kwasa-kwasan ...
23/09/2025

Tech Update;

🎓 Google Ta Yi lunch din AI Free Courses tare da Certificates 2026

Google ta ƙaddamar da sabbin kwasa-kwasan Artificial Intelligence (AI) kyauta, ciki har da Google AI Essentials da Generative AI Certificate ga ɗalibai da professionals.

Fa’idojin wannan shine :

✅ Kyauta gaba ɗaya
✅ samun damamar kin aiki da skills
✅ samun Certificate bayan kammalawa

👉 Rijista: https://tinyurl.com/5h9b4mhp

📰 A cewar Google Cloud, wannan shirin zai taimakawa matasa su koyi AI don aiki, kasuwanci, da sabbin damarmakin aiki.

Tana Shekaru 93, Dr. Ruth Gottesman Ta Ba Da Gudummawar Dala Biliyan Ɗaya Ga Dalibai Masu Karatun Likitanci Kyauta Har A...
22/09/2025

Tana Shekaru 93, Dr. Ruth Gottesman Ta Ba Da Gudummawar Dala Biliyan Ɗaya Ga Dalibai Masu Karatun Likitanci Kyauta Har Abada

Duniya ta yi mamaki lokacin da aka bayyana cewa Dr. Ruth Gottesman, mai shekaru 93, ta ba da gudummawar da takai dala biliyan 1 ga Albert Einstein College of Medicine dake New York. Wannan gudummawar dai ta sa ɗaliban makarantar ba za su sake biyan kuɗin makaranta ba — har abada.

Abin burgewa ma shi ne yadda ta yi hakan cikin tawali’u, ba tare da ta nemi a gina gini da sunanta ko a ɗora wani allon yabo ba.

Burinta ɗaya shi ne: ta dauke nauyin kuɗin makarantar da ya dade yana hana matasa masu burin zama likitoci cimma mafarkinsu.

Wannan kyauta za ta buɗe ƙofofi ga ɗalibai isa kowane matsayi na rayuwa, musamman waɗanda ba su da hali, ta kuma ba su damar shiga harkar likitanci ba tare da tsoran rashi ba.

Dr. Gottesman ta nuna cewa tasiri yafi suna.

Kuna ganin za'a iya samun irinta a Nigeria kuwa?

Ku fada mana ra'ayinku a comment section

Technology updatesWani dalibi dan shekara 19 Simon Petrus,  daga kasar Namibia 🇳🇦ya bawa duniya mamaki bayan ƙirƙirar wa...
22/09/2025

Technology updates

Wani dalibi dan shekara 19 Simon Petrus, daga kasar Namibia 🇳🇦ya bawa duniya mamaki bayan ƙirƙirar wayar da bata buƙatar SIM ko network wajen yin kira — tana amfani da radio frequency ne kawai. 📡📞

An gina wayar gaba ɗaya daga tsoffin kayan lantarki, ciki har da tsohuwar talabijin da sassan rediyo. Wannan na’ura zata ba da damar sadarwa har a wuraren da babu layin waya, babu hasumiya, ko kuma ba katin waya. Wannan na iya sauyawa mutanen karkara rayuwa inda Babu maganar farashin Kira yayi tsada ko kuma Babu service.

Bugu da ƙari, ya hadawa wayar kyamara, da fitila, da USB wajen cajin waya — duk ba tare da amfani da SIM ko network ba. wannan Abin da ya fara shi ne a matsayin gwajin kimiyya da ake bawa dalibai a makaranta, yanzu haka Wannan yaro shi yake trending a social media.

Sannan Wannan fasahar tashi ta fito a lokacin da ake bukatar ta— kuma ta zama hujja cewa lallai fasaha bata da iyaka 🌍✨



Digital MuktarDigital Muktar

Da Dumi Dumi🚨 Elon Musk Ya Fusata Kan Batun H-1B Visa! 🚨Elon Musk ya fito fili yana karfafa shirin H-1B visa, "wanda kam...
21/09/2025

Da Dumi Dumi

🚨 Elon Musk Ya Fusata Kan Batun H-1B Visa! 🚨

Elon Musk ya fito fili yana karfafa shirin H-1B visa, "wanda kamfani yiwa ma'aikaci kafin ya dakko shi daga wata kasa", inda ya ce zai “faɗa” da masu s**ar lamarin

Wannan ya biyo baya ne bayan gwamnatin Trump ta sanya sabon kuɗin visar $100,000 ga duk mai neman H-1B – abin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a fadin Amurka.

👉 Musk ya ce shirin yana kawo manyan masu hazaka daga kasashen waje, wanda bai kai ba baza a dakko shi don yayi aiki har ayi masa visar $100k ba, ya kuma ce shirin zai inganta kirkire-kirkire da ci gaban fasaha.

👉 Masu adawa kuma suna cewa hakan zai tauye hakkin mutane da rage musu albashi tunda idan kamfani ya biya $100k Don yayiwa mutum visa toh sai ya cire a cikin albashin sa.

Me ra'ayinku game da wannan kudi da aka karawa visa sai kace ta shiga aljanna? 🤔

Da Ɗumi Dumi Kamfanin SpaceX na Elon Musk ya nemi izinin ƙara tauraron dan adam har 15,000 domin bunƙasa sabis ɗin Starl...
21/09/2025

Da Ɗumi Dumi

Kamfanin SpaceX na Elon Musk ya nemi izinin ƙara tauraron dan adam har 15,000 domin bunƙasa sabis ɗin Starlink da zai rika bada intanet kai tsaye ga wayoyin salula. Wannan zai taimaka wajen samun saurin intanet kamar 4G ko a wuraren da babu layin sadarwa.

Digital Muktar

🚨 Ɗiyar Bill Gates ta Kafa tarihi wajen tsayawa da kafarta a kasuwanci! 🚨Phoebe Gates, ɗiyar shahararren attajiri Bill G...
21/09/2025

🚨 Ɗiyar Bill Gates ta Kafa tarihi wajen tsayawa da kafarta a kasuwanci! 🚨

Phoebe Gates, ɗiyar shahararren attajiri Bill Gates, tare da abokiyarta a Stanford University Sophia Kianni, sun kafa wani sabon kamfani na AI fashion-tech mai suna Phia.

A watan Afrilu da ya gabata aka ƙaddamar da shi, kuma yanzu haka sun tara dala miliyan 8 daga masu saka jari fitattu kamar Hailey Bieber, Kris Jenner, Sheryl Sandberg, Sara Blakely, da Kleiner Perkins.

Ko da yake mahaifiyarta da mahaifinta Melinda French Gates sun ki bayar da kuɗi, sun ta jaddada cewa: nasara tana tana zuwa ne bayan jajircewa da Kuma hada Kai a kunyance, ba wai suna ko kuɗin iyaye ba. 👏

Yanzu kamfanin Phia tana da masu amfani fiye da 500,000 tare da haɗin gwiwa da fiye da 5,000 fashion brands. 👗✨



Me zaku ce kuna tare da Professor Isa Ali Pantami ko Kuma kuna layin connection ?

Ku fada mana ra'ayinku a comment section

Digital MuktarDigital Muktar

Kamar yadda aka soke zaɓen Aishatu Binani, aka cire sunan Maryam Shetty acikin jerin ministoci, hakazalika “European Ame...
21/09/2025

Kamar yadda aka soke zaɓen Aishatu Binani, aka cire sunan Maryam Shetty acikin jerin ministoci, hakazalika “European American University” ta soke digirin karrama mawaƙi Dauda Rarara 🥲

A ɗakin hotel fah aka bashi wannan karramawar

Yan wanki da guga, ku mayar masa da kuɗinsa kawai shine zance 🙌

(Dr.)Rarara

21/09/2025

Wanne yafi muhimmanci iPhone 17 air ko kudin ka

20/09/2025

The reality behind iphone 17 air
5 reason that can change your mind

Da Dumi DUMI🚨 Sabon labari daga Meta!Mark Zuckerberg ya gabatar da Meta Ray-Ban Display Glasses mai farashin $799 – taba...
20/09/2025

Da Dumi DUMI

🚨 Sabon labari daga Meta!

Mark Zuckerberg ya gabatar da Meta Ray-Ban Display Glasses mai farashin $799 – tabarau mai fasaha na farko da ke da ke da display a ciki. 🤯

Ana sarrafa shi ta hanyar neural wristband technology, wato kana iya amfani da shi da nuni da hannunka kawai.

A wani videon talla da kamfanin meta ya saki a YouTube wanda bada jimawaba s**a goge shi, wanda hakan ya jawo Cece-kuce kan wannan sabon wearable tech din. 🔥

Tambaya nan shine zako ka iya siyan irin wannan tabarau idan ta iso kasuwa? 👓

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Digital Muktar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Digital Muktar:

Share

Category