08/12/2021
Mu gogaggun yan siyasa ne, ba a bakin t**i muna tsinci siyasa ba -- Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa ya dauki tsawon shekaru sama da 40 yana cikin harkokin siyasa, bugu da kari ma ita ya karanta a jami'a kuma yanzu ma ita yake yi, saboda haka ya goge a cikinta, yasan yadda ake samun rarrabuwar kai a siyasa, wanda ba sabon abu bane, kuma azo a daidaita ma ba sabon abu bane, domin ba'a daukar mutum a matsayin makiyi na din-din-din, sai dai ma ace amini na har abada.
Nasara Radio (Amanar Talaka) ta rawaito cewa, gwamna Ganduje ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da sashen Hausa na Rediyo Faransa, biyo bayan rikicin cikin gida da ta mamaye jam'iyyarsu ta APC a jihar Kano, tsakanin tsaginsa da kuma tsagin tsohon gwamna, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, wanda har ta kai ga wata kotu a Abuja ta rushe zaben mazabu na tsagin Ganduje, ta kuma tabbatar da shugabancin tsagin Shekarau karkashin Ahmadu Haruna Dan Zago, hukuncin da tsagin Shekarau s**a ce yayi awon gaba da kujerar tsohon shugaban jam'iyyar, Alhaji Abdullahi Abbas.
Ganduje yace ana nan ana sasantawa, kuma tuni uwar jam'iyyar APC ta kasa ta shiga maganar, yace suna fatan hakonsu zai cimma ruwa, domin ita siyasa tana bukatar hakuri, idan an samu sabani to sai kuma azo a shirya, a cewarsa. Sai dai kuma wasu na ganin kalaman magoya baya na kara kunna wutar rikicin, k**ar a baya bayan nan anji muryar shugaban karamar hukumar Ungoggo, Injiniya Garba Ramat, yayi kausasan kalaman akan tsohon gwamna Shekarau da sauran yan tawagarsu.
Ya kuka kalli wannan batu?
Nasara Radio 98.5 FM
8/12/2021