18/07/2025
Jihar Gombe ta Zama ta 7 a Rahoton Jihohi Mafiya Ƙoƙari na Bana
Daga Aliyu Bala Gerengi a Gombe
Jihar Gombe ta sake samun karramawar ƙasa a matsayin abar koyi a fagen shugabanci na gari, da sauye-sauye da kuma muhimman harkokin ci gaba, inda ta samu matsayi na 7 a ƙasa baki ɗaya a bana, a rahoton ƙoƙarin jihohi na ‘Phillips Consulting State Performance Index’ inda ta yiwa jihohi 30 fintinkau a faɗin ƙasar nan.
Cikakken bayani a Rahoton ƙoƙarin Jihohin na bana, sakamako ne na binciken da babban kamfanin ƙwararrun masana, Phillips Consulting ya tattara, ɗaya daga cikin nagartattun cibiyoyin bincike da ƙididdiga masu ƙima a Najeriya.
Binciken ya sanya jihohi 36 da Abuja a kan wassu ma'aunai masu mahimmanci da s**a haɗa da mulki, tattalin arziki, ci gaban zamantakewa da samar da ababen more rayuwa.
A yawancin waɗannan batutuwan da aka auna, Jihar Gombe ta yi rawar gani tare da samun gamsuwa daga al’ummarta.
Jihar ta zo ta ɗaya a fannin ingantattun hanyoyi da kulawar jinya a asibitocin gwamnati, hakan ya nuna ƙarara irin jajircewar gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa da inganta lafiya.
Har ila yau, jihar ta zo ta 1 a fagen Sauƙaka harkokin Kasuwanci, lamarin dake nuna kyakkyawan yanayi mai haba-haba da masu zuba jari da hukumomi masu nagarta.
Har ila yau, Gombe ta zama ta 2 a fannin Tsaron Rayuka da Dukiyoyi da Tsaftar Muhalli, wanda hakan ke nuni da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban al’umma.
Sauran sassan da Jihar Gomben ta yi fice sun haɗa da: zuwa matsayi na 3 a fagen Taimakekeniyar Lafiyar Jama’a – biyo bayan nasarar aiwatar da shirin inshorar lafiya na Go-Health, da kuma zuwa matsayi na 5 a fannin Sufuri da Ilimi, lamarin dake tabbatar da ƙaruwar tallafi ga talakawa da marassa galihu.
Rahoton ya alaƙanta wannar nasarar da himma da jajircewar Gwamna Inuwa Yahaya, da salonsa na gudanar da mulki daya karkata ga muradun jama’a, da kuma ci gaba da kawo sauye-sauye.
Rahoton ya yi hasashen cewa an ɗora Gombe kan