12/05/2023
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Daga:- Ahmed Habib Yauri
Director General Media and publicty.
Kungiya Zabarmawa wato ZADA ZABARKANA tana sanar da dukan Zabarmawa na cikin kasa (Nigeria) da sauran kasashen waje cewa ta fara raba form na shiga wannan kungiya.
ZADA ZABARKANA kungiya ce da aka kafata domin cigaban dukan Zabarmawan duniya baki daya, Babban manufar ta shi ne hada kan Zabarmawan duniya baki daya da Kuma bunkasa yaren Zabarmanci ta yanda zata dinga gogayya da sauran manya-manyan yarukan duniya.
Kada ka bari a barka a baya matukar kasan cewa Kai Bazabarme ne ko daga ina kake a fadin duniya, ko da baka jin yaren muddin dai Kai din Bazabarme ne yi maza-maza ka yi register da wannan kungiya domin ka kasance cikin members na wannan tafiyar.
Mallakar wannan forms ne zai baka damar zama halstaccen 'dan kungiya tare da samun I.D card na kungiyar ZADA ZABARKANA.
Hanzarta ka mallaki naka Form din a wajen Chairman din kungiyar na State/chapter din da kake a fadin Nigeria baki daya. Ko Kuma ka ajiye number ka domin shiga Whatsapp group din domin samun Karin bayani.
Ku yi sharing domin sauran Zabarmawa su gani.