Muhammad Sanusi ll Legacies Initiative.

Muhammad Sanusi ll Legacies Initiative. Motto: service to humanity.
(1)

24/05/2025

Yanzu haka Fitowar Mai Martaba Sarkin Kano Mal Khalifa Muhammadu Sunusi na ll Phd Con. Ya Fitowa Domin Zaman Addu,a Ta Cika Shekara Daya da Dawowar Sarki Kan Karagar Kujerar Mulkin Kano, Mai Martaba Sarki ya Masu Bakuncin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.

Muna Addu,a Allah ya taimaka Sarki Allah ya Karawa Sarki Lafiya Allah ya karya Makiyan Sarki Allah ya Zaunar da Kano Lafiya Duk Me Neman Kano ta Wata Fitina Allah ya Mayar Masa Kansa Ameen.

Sanarwa Daga Nakowa Media✍️

Da dumi'dumi: Iyalan Ganduje sun yi watsi da Aminu Ado Bayero, sun yi wa Sanusi II mubaya'a amatsayin Sarkin KanoJaridar...
14/05/2025

Da dumi'dumi: Iyalan Ganduje sun yi watsi da Aminu Ado Bayero, sun yi wa Sanusi II mubaya'a amatsayin Sarkin Kano

Jaridar Guardian Nigeria ta ruwaito cewa Bayan da aka dauki tsawon lokaci ana takaddama a masarautu, a karshe dangin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun amince da Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Baya ga haka, tsohon Gwamna Ganduje ya amince da nadin dansa Alhaji Jamilu Sani Umar, a gaban fadar Sarki Sanusi da aka nada a matsayin Hakimin Ganduje na karamar hukumar Dawakin-Tofa a jihar Kano.

A wani gagarumin biki da ya gudana a fadar Kofar Kudu, Sarki Sanusi ya nada dan uwan ​​Ganduje, Alhaji Umar, a matsayin sabon Hakimin kauyen a cikin dimbin jama’a daga Ganduje wadanda s**a sabunta biyayya ga Khalifa Sanusi.

Bugu da kari, ci gaban da ke kunno kai, wanda ya sake bayyana mubaya’ar Ganduje da iyalansa a siyasance, a karshe ya yi watsi da irin goyon bayan da jiga-jigan jam’iyyar APC ke yi na tsige Aminu Ado Bayero.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan uwan ​​Ganduje sun taba tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan tsige Sarki Sanusi na 2020 a lokacin da dansu (Abdullahi Umar Ganduje) yake Gwamna.

Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD CON, ya halarci taro a matakin Duniya kan bunkasa zuba jari da Kasuwanci na A...
07/05/2025

Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD CON, ya halarci taro a matakin Duniya kan bunkasa zuba jari da Kasuwanci na Africa a kasar Tunisia

Hajjin bana: Sarki Sanusi ya bukaci da a dawo da nadin Amirul Hajj na ƙasa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanus...
01/05/2025

Hajjin bana: Sarki Sanusi ya bukaci da a dawo da nadin Amirul Hajj na ƙasa

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba yiwuwar dawo da nada Amirul Hajj na Kasa, k**ar yadda aka saba a baya.

Sarkin ya bayyana hakan a yau lokacin da ya karɓi bakuncin jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano a fadarsa, in ji nasarar da kakakin hukumar alhazai ta Kano, Suleman Dederi ya fitar.

Sarkin ya jaddada muhimmancin dawo da tsarin zabar Amirul Hajj na Kasa, wanda zai jagoranci tawagar Najeriya a lokacin aikin Hajji na kowace shekara. Ya ce tsarin Amirul Hajj ya samo asali ne tun zamanin Annabi Muhammad (SAW), wanda ya karfafa nada shugabanni domin jagorantar tafiya mai tsarki irin ta Hajji.

Ya nanata bukatar sanya nada Amirul Hajj na Kasa a matsayin wani muhimmin bangare na aikin Hajji da ya zama na dindindin.

A nasa bangaren, Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce sun kai ziyara fadar sarki ne domin gayyatar Mai Martaba zuwa taron karshe na gwajin aikin Hajji da za a gudanar a sansanin Hajji.

Alhaji Lamin Rabi’u ya kara da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da s**a dace domin fara jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki, wanda za a fara ranar 13 ga Mayu, 2025.

Shima a jawabinsa, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar, Alhaji Yusif Lawan, ya nuna godiya matuka ga Mai Martaba, Malam Muhammad Sanusi II, bisa sadaukarwarsa da jajircewarsa wajen kula da jin daɗin alhazai ‘yan Najeriya. Haka kuma ya goyi bayan kiran da ake yi na neman Gwamnatin Tarayya ta dawo da mukamin Amirul Hajj na Kasa.

Hawan Babban Daki/Daushe !Saturday, 26th April 2025.
26/04/2025

Hawan Babban Daki/Daushe !

Saturday, 26th April 2025.

Ƙungiyar"Muhammadu Sanusi II legacies initative" tagabatar da taron sada zumunciƘungiyar Muhammadu Sanusi II legacies in...
21/04/2025

Ƙungiyar"Muhammadu Sanusi II legacies initative" tagabatar da taron sada zumunci

Ƙungiyar Muhammadu Sanusi II legacies initative ta gudanar da taron sada zumunci da yayan ƙungiyar dake sassa daban daban.

Taron yagudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na kasa Usman Aminu Sulaiman,a ranar asabar 20/4/2024 a Minjibur park dake karamar hukumar Minjibur jihar Kano.

Yayin taron an gudanar da Walimar cin abinci da ƙungiyar ta hada.

Yayan ƙungiyar na jihohi daban daban ne Šùķa hallaci taron inda Alhaji Usman da Alhaji Faruq Garba Sarkin Matasan Kauru s**a hallaci taron daga jihar Kaduna yayin da Aliyu Abba Daura Daga jihar Katsina dama sauran wurare da dama s**a hallaci taron.

Sign Umar Saleh Zara
National Director Media and publicity

20/04/2025
Sarkinmu abun nunawarmu a Duniya.Sarkin Kano Mallam Dr. Khalifah Muhammad Sanusi II PhD  tare da King Charles.Babu shakk...
16/04/2025

Sarkinmu abun nunawarmu a Duniya.

Sarkin Kano Mallam Dr. Khalifah Muhammad Sanusi II PhD tare da King Charles.

Babu shakka Sarkin Kano Khalifa yana da Daraja a Duniya kuma Kanawa da duk me son jihar Kano yana alfahari da wannan baiwa da muke da ita na samun Sarkin da Duniya take Kallo kuma karansa yakai Tsaiko, ko bakomai muna da Sarkin fita Kunya kuma Abun nunawarmu a Duniya.

Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD  ya halarci wani taro a birnin London, don tunawa da ‘yan Makaran...
14/04/2025

Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II PhD ya halarci wani taro a birnin London, don tunawa da ‘yan Makarantar Chibok da ‘yan ta'adda s**a sace shekaru 11, da s**a gabata, wanda Hajiya Aisha Murtala Mohammad ta shirya don tunawa da ‘yan Makarantar ta Chibok.

Dattijo Alh Aminu Alhasan Dantata Ya Ziyarci fadar sarkin Kano khalifa Muhammad Sanusi II PhD Don Ta'aziyyar galadiman K...
12/04/2025

Dattijo Alh Aminu Alhasan Dantata Ya Ziyarci fadar sarkin Kano khalifa Muhammad Sanusi II PhD Don Ta'aziyyar galadiman Kano Alhji Abbas sanusi.

Yayi Addu'a Da Fatan ALLAH UBANGIJI Ya Gafarta Masa Yasa Yana Aljanna

CONGRATULATIONS ME GIRMA TAFIDAN KANO ALLAH YA K**A
08/04/2025

CONGRATULATIONS ME GIRMA TAFIDAN

KANO ALLAH YA K**A

Congratulations mai Girma Wamaban KanoAllah ya k**a
08/04/2025

Congratulations mai Girma Wamaban Kano

Allah ya k**a

Address

Kano

Telephone

+2348037852776

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Sanusi ll Legacies Initiative. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muhammad Sanusi ll Legacies Initiative.:

Share