20/02/2026
Mutane na ganin idan ba ka da ido shi kenan ka haƙura da rayuwa… Amma labarin Mal. Murtala Haruna Abdullahi — mai larurar rashin gani kuma mahaddacin Al-Qur’ani ya nuna mana cewa nakasa ba ƙarshen rayuwa ba ne, jarabawa ce da ke ɗaga darajar bawa idan ya rungumi imani da haƙuri.
A cikin wannan shirin na Rayuwata, mun yi hira da shi domin jin labarin rayuwa mai cike da darasi, jajircewa da tawakkali ga Allah.
A yayin shirin, Chairman na Sagama Homes Ltd, Alh. Ali Nuhu, ya ba shi kyautar ₦250,000 domin ya ci gaba da inganta rayuwarsa da ayyukansa na alheri wani abin alfahari da ya nuna muhimmancin tallafawa juna da ƙarfafa masu ƙalubale a cikin al’umma.
Mun tambaye shi yadda yake haddace Al-Qur’ani da koyarwa ba tare da gani ba, sirrin nasararsa duk da jarabawa, da wace shawara yake bai wa masu irin wannan ƙalubale. Haka kuma ya yi kira ga iyaye da al’umma su ƙara tausayi da fahimta ga masu nakasa domin su zama masu amfani ga al’umma.
Amsa ta ƙarshe ta taɓa zuciya sosai me Allah yake son mu fahimta daga jarabawarsa?
Ku kalli cikakken shirin a YouTube channel ɗinmu: Tubless Media Concept.