12/06/2026
Par 3 Na so shi tsawon shekaru 10… amma daga ƙarshe ya ci amanata.
Fitacciyar mawakiya mai basira Shamsiyya Sadi ta bayyana mana yadda ta sadaukar da soyayyarta tsawon shekaru sama da 10 ga mutumin da take shirin aura… amma daga ƙarshe ya juya mata baya ya zaɓi rabuwa da ita. 😢
Ta bayyana irin kaɗaicin da ta shiga bayan ta rabu da kowa saboda shi… amma duk da haka ta tsaya da ƙafafunta, ta maida raɗaɗin rayuwarta zuwa waƙoƙin soyayya da yaudara da suke shiga zuciyar mutane.
A cikin wannan hira mai cike da gaskiya da tausayi, Shamsiyya Sadi ta bayyana:
💔 Dalilin da yasa take yin wakokin soyayya da yaudara
💔 Yadda cin amana ya canza rayuwarta
💔 Kalubalen da ta fuskanta a rayuwa
💔 Kasuwancin da take yi har ta samu tallafin ₦250,000 daga Rayuwata Talkshow
Ku kasance tare da mu domin kallon cikakken shirin nan bada jimawa ba.
YouTube Channel: Tubless Media Concept
🎥 Rayuwata Talkshow