06/12/2023
GANGANCI KO KUMA RASHIN ƘWAREWA??
Daga. Mubarak Shehu Dayyab
Acikin wani rubutu da na karanta na (U.S. Africa Command Strike Process) sunyi bayani akan hanyoyin da ake bi wajen ƙaddamar da harin jirgin sama. Kamar haka...
1: (Defensive Strike Process) wanda shine na ƙara kai daga hari, sai kuma
2: (Deliberate targeting process) wanda shine na kai wa, wato shi wannan (Deliberate Targeting process) saboda matuƙar hatsarin sa yana bukatar kwararru wajen aiwatarwa.
A lokacin kai wannan harin ana buƙatar military lawyers wajen target identification da kuma nomination process, inda military lawyers zasu conducting review akan harin da kuma inda za'a kai harin, shin gurin akwai civilians ko babu, kafin a kai wannan harin sai an tabbatar da cewa babu wani civilian a gurin, ana samun ƙwararru masu kaifin basira domin bujuro da mataki daban daban da za'a bi kamarsu, samun signal, human imagery, da open source intelligence da sauransu. A duk lokacin da aka fahimci cewar akwai civilians a gurin to ana adjusting lokacin kai harin, kokuma a canja makamin da za'a yi amfani da shi, ko kuma ayi haƙuri da kai wannan harin, har sai lokacin da aka tabbatar babu civilians a gurin. Duk da cewa wani lokaci ana samun matsaloli wajen samun bayanai da kuma kurarurai da baza a rasa ba, amma to ya abun yake ne a Nijeriya????
Shin ganganci ne ko kuma rashin sanin makamar aiki, ganin irin abubuwan da s**a faru a baya bayannan da kuma kwana kwanannan kamar haka....
2014: BORNO STATE
A cikin watan March 2014, jirgin sojoji, a ƙoƙarin sa na zakulo, yan ta'addan boko haram, a dajin sambisa, sun harba ma bayin Allah da basu ji ba basu gani ba bom a ƙauyen, Daglun a jahar Borno State. Inda hakan ya janyo rasa rayuka masu yawa. A wannan lokacin rahoton da aka bayar shine wai kuskure ne akayi, saboda anyi tunanin wani san sani ne wanda mayaƙan boko haram suke ɓuya, a wannan lokacin rahoton da CNN, ta bayar Ali Ndume, sanatan dake wakiltan wannan shiyar yace wai kuskure ne.
2017: BORNO STATE
Acikin January 2017, an sake ayyanawa jirgin saman sojoji ya ƙara sakin bomb a sansanin ƴan gudun hijira na Rann, a ƙauyen Kala-Balge, inda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da ɗari, da kuma jikkata mutane masu yawa, a wannan lokacin ma an ƙara cewa wai kuskure ne.
2019: ZAMFARA STATE
Har ila yau acikin watan April 2019, jirgin sojoji a ƙoƙarin su na ɗakile harin ta'addanci na masu garkuwa da mutane, sun kai hari a ƙauyen Tangaram, a jahar Zamfara inda haka yayi sanadiyar rasa rayuka masu yawa, da kuma jikkata wasu, a wannan lokacin ma an ce kuskure ne.
2021: BORNO STATE
Shekara hudu bayan harba bomb da akayi a sansanin a gudun hijira wanda sojoji s**a je bisa kuskure ne, sun ƙara tafka wani kuskuren wajen harbawa a kauyen, Kwatar Daban Masara kusa da Lake Chad, inda yayi sanadiyar mutuwar a ƙalla fiye da mutane 20 masu kamun kifi sun mutu inda da yawa s**a jikkata.
2022: YOBE STATE
Har ila yau acikin watan September 2021, a ƙoƙarin sojojin Nigeriya na yaƙar yan ta'adda sun ƙara harba wani bomb a ƙauyen Buhari dake Yobe, inda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da Goma da jikkata mutane sama da ashirin.
Inda a sanarwar su sun tabbatar sunga wurgawar yan ta'addan boko haram a yankin Kudancin Kanama, kasancewar yankin yana fama da matsalar ta'addanci.
2022: KATSINA STATE
Acikin watan July 2022, jirgin yaƙi na Sojojin Najeriya ya ƙara jefa bomb a ƙauyen Kunkuna ƙaramar hukumar Safana a jahar Katsina, inda yayi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa da kuma jikkata wasu. Inda rahoto ya bayar hakan yafaru a bisa kuskure ne wai, wajen ƙoƙarin su na kaima ƴan ta'adda hari.
2023: KADUNA STATE
Ranar 4 ga watan December, sojojin Nijeriya sun ƙara harba bom a wani ƙauye me suna tudun ɓiri inda jama'a suke yaran maulidi na shekara, inda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da ɗari da kuma jikkata mutane masu ɗimbin yawa, acikin rahoton da sojojin s**a bayar sunce hakan ya faru bisa kuskure ne.
Note:
Shawara itace yakamata a samu ƙwararru wanda s**a san makamar aiki, ba yaƙi da jiragen sama a ɓangaren sojojin saman Najeriya wanda zasu bada horo da kuma bayanai masu inganci wajen ganin an magance wannan matsalar, da kuma ƙara lura da kulawa da kayan aiki, wato jiragen da ake fita dasu ƴaki wajen ganin suna da isasshen lafiya, domin kaucewa afkuwar irin wannan matsalar nan gaba.
Allah ya jiƙan ƴan uwan mu wanda s**a riga mu gidan gaskiya. Ameen.