10/07/2025
Tarihin Pi Network (1)
Pi Network an kaddamar da ita a ranar 14 ga Maris, 2019 — wato Pi Day — domin nuna alaƙa da lambar lissafi π (3.14). A lokacin ƙaddamarwa, an saita yawan hakar kudin Pi a kimanin 3.14 Pi a kowace awa. Wato, a cikin awa 24 na rana, za a iya samun kusan Pi 75 (3.14×24) daga aikin Mining. Wannan yawan ya dace da lambar π, domin 3.14 awa ya zama kimanin 75 a rana.
Bayan haka, yawan Pi da ake samu ya ragu a hankali yayin da yawan masu hakar ya ƙaru. Misali:
Afrilu 2019 (masu yin Mining sun kai 1,000): Yawan hakar ya ragu zuwa kusan 1.6 Pi a kowace awa.
Mayu 2019 (adadin masu yin Mining sunkai 10,000 ): An sake ragin yawan hakar zuwa ~0.8 Pi a kowace awa.
Yuli 2019 (adadin masu yin Mining yakai 100,000 ): Yawan hakar ya zama ~0.4 Pi a kowace awa.
Wannan tsarin raguwar hakowa (halving) an saita shi ne domin a rage yawan Pi da ke fita yayin da jama’a ke ƙaruwa, k**ar yadda aka tsara a farko.
Kalubale a Farko
A farkon zamanin hakar Pi, an fuskanci ƙalubale da dama:
Rashin fahimta: Wasu sun yi zargin cewa tsarin gayyatar jama’a na Pi ya yi k**a da tsarin tallace-tallace na matakai da yawa (MLM). Wannan ya sa mutane da dama s**a fara zargin cewa aikin na iya zama na ruɗani.
Jinkirin fitar da mainnet: An yi alƙawarin ƙaddamar da babbar hanyar sadarwa (mainnet) na Pi, amma sai shekaru da dama s**a wuce kafin hakan ya faru. Wannan jinkiri ya haifar da rashin jindadi da haƙuri a tsakanin masu amfani.
Rashin bayanai: Ba a fayyace yadda tsarin Pi Network yake aiki ko yadda za a rarraba kudaden ba. Babu cikakken bayani (white paper) da ke nuna yadda za a fitar da Pi, don haka mutane da dama sun taru cikin ruɗani kan gaskiyar aikin.
Shin kai ma kana da Pi?