
18/07/2025
Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban bankin aikin gona
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Muhammad Babangida, dan tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, a matsayin shugaban Bankin Cigaban Aikin Gona da aka sauyawa fasali.
Sanarwar nadin ta fito ne a ranar Juma’a, tare da nadin wasu mutum bakwai da za su jagoranci wasu manyan hukumomin gwamnatin tarayya daban-daban.
Muhammad Babangida, wanda ke da shekaru 53, ya samu digiri a fannin Gudanar da Kasuwanci da kuma Huldar Jama’a daga Jami’ar Montreux, Switzerland. Haka kuma, ya kammala wani shirin horo a kan shugabanci da tafiyar da kamfanoni a makarantar koyar da harkokin kasuwanci ta Harvard Business School a shekarar 2002.