02/08/2024
🚨| Yana da kyau idan da hannun ka a kona Digital Industrial Park (DIP) Nigerian Communication Commission (NCC) ka san wannan.
DIP NCC daya ce daga cikin centres guda shida da aka gina a NIGERIA. Kowane zone da ke kasar nan an kai musu guda daya. A northern states, Kano ce kadai ta samu.
An samar da center din ne don promoting digital economy and entrepreneurship for northern youths. Anan ne ake sa ran kaddamar da Data Centre ta farko a northern Nigeria. Wanda zata iya kawo wa Kano Haraji da kudin shida sama da million dari uku duk wata.
Aikin da akai a gurin, da systems da aka zuba, da servers, da devices da configurations din CISCO ne s**a zo daga America s**a yi. Na tabbata idan ba babban rabo ba da kuma ikon Allah, wannan gurin bazai tashi ba. Shikenan an rufe babin sa. Sabida billion dollar project ne.
A yadda plan din yake DIP centre zata samarwa da Kano ma'aikata akalla dubu goma sha. Wannan wuri zai zama wuri na farko a arewa da yan arewa zasu amfana da shi wajen koyan advanced networking, cloud computing, data science da Business Analytics.
📍 Idan zuga ku akai, to an cuce ku, idan kuma kwakwalanku ne, kun cuci kawunan ku. Domin kuwa salary din mutum daya a wajen zai iya kula da yan gidan ku mutum goma. A karshe aikin assha da ku kayi yayi costing ma Kano wannan opportunity din da Jobs da kuma revenue.
Ina tunani anan?
Don Girman Allah kuyi sharing don su gani. Su kuma san me su kayi.
Muhammad Ubale Kiru