11/09/2021
SHIGA YAJIN AIKI A WANNAN LOKACI DA ƳAN-NAJERIYA SUKAFI BUKATAR KU BASHI NE MATAKI DA YA KAMATA KU DAUKA BA, SHUGABA BUHARI YA FAƊIWA LIKITOCI.
Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Juma'a a Abuja, yayi kira ga Ma'aikatan jinya da su komo bakin aikin su, ya bukaci Sauran masu tunanin tsunduma yajin aiki kan su zabi yin sulhu ta hanyar tattaunawa, komi tsawon lokaci da hakan zai dauka.
"Rayuwar mutane da za'a iya rasawa ko lalatarwa idan Likitoci s**a janye aikin su, sun isa susa azabi hanyar lumana da samun mafita akan Banbance Banbance dake tsakanin," Shugaban kasa ya nunar da Hakane, a yayin daya karbi Membobin Ƙungiyar likitoci ta Ƙasa (NMA) a fadar Gwamnati.
Shugaba Buhari ya bada tabbaci cewa za'a bisa dukkan hakkoki likitocin da suke bi, bayan an kammala tantancewa, ya nunar da cewa tsunduma yajin aiki a wannan lokaci Muhimmi da bukatar lafiya ga Ƙasar da Ƴan-kasa ba abu ne daya dace ba.
"Bada kariya ga Ƴan-Kasar mu ba abu ne daya kamata abar gwamnati ita kadai akai ba, abune da zamu dauka hakkin sa gaba da yan mu, wanda musamman kwararru a Fannin lafiya ke taka muhimmin rawa. Bari na fada kai tsaye wa likitocin dake yajin aiki, matakin tsunduma a dai dai wannan lokaci da Ƴan-Nijeriya ke bukatar ku fiye da kowani lokaci ba mataki ne daya dace ku dauka ba, koma wace irin sabani aka samu.
"Wannan Gwamnati tanada ƙyaƙƙyawan tarihi na biyan dukkanin bashi da ma'aikatan gwamnati ke binta, Ƴan fansho, da Ƴan kwangila kuma mun waiwayi bashi da Gwamnatocin baya s**a bari, da zarar an tantance duk abinda ya kamata bisa ka'ida, bashi na gaskiya da ma'aikatan jinya ke bi za'a biyasu.
“Na fahimci cewa wasu cikin Manyan bukatu goma sha biyu 12 na yajin aiki da akeyi abune da tuntuni an magance su. Duk da de abun sake dubi kan alawus na aiki kan hatsari ba'a tattauna sosai yadda ya kamata akai ba saboda yana yin dake ciki na likitoci dake yajin aiki."
Shugaban Ƙasa Buhari, yace matsala da dama kenan wanda Shugaban Ma'aikata ya miƙa saikula akai, kan batun cire abinda ake kira (House Officers) da cire likitoci daga shirin Bautar ƙasa na NYSC an karashi cikin batun da aka tura ga Hukumar Kula da daidaita albashi na ƙasa don tayi karin haske cewa za suci gaba da samun albashi harda tsarin kari kan bukatun su, sama da yawan wanda s**a saba samu.
Ya kara da cewa "Na bukaci cewa yarjejeniya da aka cimma a taron da akayi ranar 20th da 21st ga watan Ogusta dake cikin yarjejeniyar wanda na gani an fara aiki dashi,".
Don kara inganta Sashin lafiya, Shugaban kasa yace, an kara yawan kasafin kudi kuma an kaddamar da Kwamitin gyara sashen lafiya, karkashin Ma'taimakin Shugaban kasa, domin gano da magance inda ake da naƙaso a tsarin lafiya da yin daidaito da tsarin aiki mai kyau irin na ƙasashen Duniya, wanda jama'a s**a gamsu dashi.
"kuma muna Tallafawa shirye shirye don faÉ—aÉ—a inshuran lafiya da samar da karin kuÉ—aÉ—e ga Sashin lafiya.
“Muna da kalubale da yawa dake gaban mu da abubuwa da dama da zamuyi, ga Ɗunbin jama'a da muke dasu,
Ya kara da cewa "Don haka, ya dace na tunatas daku cewa, a matsayin ku na Manyan Ma'aikatan Jinya kuma Wakilai na daya cikin kungiyoyi dake da ƙima sosai a Duniya, Hakki dake wuyan ku karara yake na wanzuwan Ƴan-Nijeriya cikin lafiya.
"Bai kare kawai kan batun abubuwan walwalar membobin ku ba, amma abune daya kunshi ci gaba da sauke nauyi dake wuyan ku ga dukkan kasa baki daya, da fannin lafiyar da daidaituwar Al'amuran Kasar,".
Shugaba Buhari, yayi nuni da cewa hanyoyin tattalin arzikin Najeriya sama da Shekaru yana raguwa a hankali, hankali, tare da karuwar yawan Al'umma.
"Annoba Korona ya shafi Tattalin arzikin Duniya, duk da labarin mai dadin daya faru Ƴan kwanakin nan, na samun haɓakan tattalin arzikin Najeriya da sama da kaso biyar cikin watanni uku da s**a shuɗe, har yanzu akwai kalubale da muke son ganin mun magance kan asusun Kasar, kamar dai Sauran kasashe.
Shugaban kasa yace "Hanyar samun kudin shiga da Najeriya ta dogara dashi tsawon lokaci yana fiskantar koma baya a duniya, yawan Al'umman mu na karuwa ba dare ba rana, tashin hankali dake tattare da haka na karuwa daga kowani Bangaren, hakan na kara sanya matasa tsunduma cikin fitintunu.
Ƙungiya kamar ta likitoci NMA zata iya taka rawa mai Imfani da zai kawo daidaito a cikin zaman takewa,"
Shugaba ya yaba da irin aiki cigaba da kungiyar likitocin ta Ƙasa take taka wa, a matsayin ta na babbar kungiyar Ma'aikatan lafiya, musamman kan abinda ya shafi yajin aiki dake gudana.
"Wannan Shine rawar daya kamata kungiyar ta NMA ta taka, a matsayinta na kungiya mai Dattako, wanda membobin masu kamala da gogewar aiki ke jagoranta.
"Ina kuma alfahari da fahimtar cewa an samu cigaba matuka a asibitocin mu, kamar na raba tagwaye da aka haifa a like da juna, da kokarin Ma'aikatan mu na sashen lafiya Gurin tafiyar da Annobar Cutar Korona, Wanda abinda s**a yi ya janyo mana daraja a nan gida da kasashen ke tare, da bada gurbin aiki da akayi kwanan nan, ga daya daga cikin Abokan aiki a mukamin Ma'taimakin Babban Darakta a Hukumar Lafiya ta Duniya, har wayau Muna kara taya murna wa Dakta Chikwe Ihekweazu kan samun wannan mukamin."
Shugaba Buhari ya aiyana cewa Illar da Cutar Korona ta jefa Najeriya ciki har yanzu ba'a kammala goge shi ba, kana kuma dole mu hada kai Gurin magance ta.
Cikin jawabin sa, Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire, yace kungiyar NMA yana taka muhimmin rawa ga Cigaban sashen lafiya, musamman Gurin magance Annoba, aiki guri daidaituwa da lafiyan Al'umma.
Shugaban Ƙungiyar Likitoci NMA, Farfesa Innocent A. Ujah, ya godewa Shugaban kasa, na nadin membobin kungiyar a Muhimman matsayi a gwamnati, da amincewa da shirin, Medical Residency Act and immunization coverage.
Shugaban NMA, yace kungiyar ta damu da yajin aikin da likitoci s**a tsunduma, kuma yana iya kokarin don ganin an rage sassauta halin da majinyata suke ciki a Fadin ƙasa, yayin kuma ya Roki a samu sasanci cikin kankanin lokaci.
Shugaban Ƙungiyar NMA, ya godewa Shugaba Buhari, bisa kafa Jami'an Kimiyyan Lafiya a Karon farko a Otukpo jihar Benuwe, da Azare, jihar Bauchi da Ila Orangun, jihar Osun, Shugaban Ƙungiyar ya miƙa bukatar Samar da kudade da s**a dace ga Sabbin Jami'oin.
Ya tabbatar wa Shugaban kasa, cigaba da samun goyon baya na membobin kungiyar don kara inganta sashen lafiya a Ƙasar.
Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama'a.
10th ga watan Satumba, 2021