02/06/2025
Assalamu alaikum warahmatullah.
A madadin mu al'ummar Garin Kadawa Miltara baki ɗaya muna kira ga Mai girma Gwamnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusif . bisa wannan barazana ta zaizayar ƙasa data daɗe tana ci mana tuwo a kwarya.
Wannan shine kwari ko zaizayar ƙasa da take faruwa a Unguwar Kadawa Miltara dake ƙaramar hukumar Ungoggo a nan Jihar Kano,kuma haƙiƙa wannan zaizayar ƙasa ta ɗauki tsawon lokaci tana cin filayen mutane har ma da gidaje kuma yanzu haka tana cigaba da tafiya.
A duk shekara wannan zaizayar ƙasa tana wahalar da mutanen wannan yanki ,kuma fiye da kashi 99 na mutanen wajen mutane ne masu ƙaramin ƙarfi . Wlh duk wanda yaga yadda wajen yake zai mutuƙar tausayawa.
Musamman yadda mutanen unguwa suke haɗa kuɗi su sayi ƙasa da Dutse a kowacce shekara dan su tsira daga wannan mummunar zaizayar ƙasa, Amma duk da haka kafin Damina ta wuce sai wannan zaizayar ƙasa tayi ɓarna An samu rushewar Gidaje da tsatstsagewar layukan unguwar. 😭😭
Haƙiƙa wannan wuri yana mutuƙar bukatar Taimakon gaggawa daga Gwamnati Sakamakon irin barazanar da take tattare da wajen , domin wurare irin waɗannan banda barazanar zaizayar ƙasar ma sukan zama mafaka ta aikata abubuwan da basu dace ba.
Muna Kira Ga mai girma Gwamnan Jihar Kano Ramadanan Gwamna mai Adalci da son cigaban jihar Kano daya Dubi wannan matsala da muke ciki ya kawo mana ɗauki sakamakon shigowar Damina, domin wannan shine lokaci mafi haɗari ga yankin.
Mai girma Gwamna Muna addu'ar Allah yasa wannan sako ya isa gareka Allah ya ƙara maka lafiya da kwarin gwiwar cigaba da malala Ayyukan Alkhairi a Jihar mu ta Kano mai albarka
Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya 🤲🤲
KADAWA MU FARA. 📢
KADAWA YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION. 📢