15/10/2025
EMOTIONAL CONTROL
RISK
SET-UP
KULA DA KAYA......
Shawara da zan bawa kowa ma duk wani me irin wannan matsalar shawara UKU zan baku IN SHAA ALLAHU zaku rage yawan duba charts da yanke hukunci wanda be dace ba
1~ ka tabbatar ka saka kudi wanda kasan kafi ƙarfinsu, kudi wadanda kasan idan ka saka koda ka rasasu bazaka shiga damuwa ba
Misali idan Kanada ₦50k a account ɗinka idan kanaso kayi depositing wannan kudin ka fara trading dasu
Abinda zakayi kada kayi p2p da wannan ₦50k ɗin saboda ita kadaice a cikin account ɗinka, kaga kenan zaka saka buri akanta,
Abinda zakayi ka fara depositing ₦10k a wallet dinka, saika siya dala da ita misali ka sama $10 to wannan $10 saika dauka itace Capital dinka na trading saika tsara mata Risk management daidai gwargwado yanda zatayi lasting
2~ Ka tabbatar ka sama entry me kyau, ka natsu da kyau ka tabbatar entry daka shiga yanada inganci koda signal aka baka kasan irin abinda Yakamata kayi da Dukiyarka, aƙalla ka duba trade sau biyar kafin ka shiga don ka tabbatar ka sama entry me kyau,
Hakan zaisa koda wayarka bata kusu dakai zaka rinka saka hope akan trade daka shiga, ba canki canki kayiba, kanada yaƙina akai
3~ ka tabbatar duk trade da zaka shiga, kasan wajan shiga da wajan fita, Indai ba holding kakeyi ba, to ka tabbatar ka saka TP da SL sannan dolene ka tabbatar ba FOMO kahau ba, saboda majority hawa FOMO ba'a saka SL saidai TP saboda babu wajan saka SL, Ka kiyaye FOMO, SABODA AKWAI coins SUNFI 1M a kasuwa idan wannan ya wuce ka ka nema wani ka jira,
Saka TP da SL shine zaisa KO kana bacci bazaka rinka tuna cewa akwai wata matsala ba, dama kasan DUBAI KO DAWANAU.
_____
Inda matsalar take shine, matsalar mu dogon buri
Muna saka kudi wanda idan muka rasa zamu daura hannu akai muyita salati
Mutun daga yaga set-up kokuma yaga an kawo signal burinshi ya shiga baya tunanin abinda zai rasa saidai abinda zaka samu.
Mutunne yanada ₦100k a account sai yaga an kawo signal babu dubawa, kawai sai yayi p2p da 90k kokuma ma duka kudin saboda son banza da dogon buri
To tayaya zakayi bacci kenan, bayan ko kudin karyawa da safe baka rage ba, kana tunani da saƙe saƙe
Dolene nu cire dogon buri
Dole ne mu zama masu kare dukiyar mu
Ka rinka tuna wahalar da kasha kafin ka sama wannan kuɗin ka saka a trading
____
Sannan a rinka haɗawa da addu'a kowani lokaci.
BARKA DA DARE,
Kada a manta ayi sharing saboda wasu su amfana.
✍️✍️Ismail IBN Abdullah✍️✍️