05/09/2025
Zan iya barin NNPP – Inji Dan Majalisa Abdulmumin Jibrin Kofa
Abdulmumin Jibrin, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji kuma na kusa da Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai kamata a dauki abin mamaki ba idan ya bar jam’iyyar.
Ya ce kuma ya isa ya dauki matsayar kansa a siyasa bisa abin da ya ga ya fi masa alheri.
Yayin da yake zantawa da DCL Hausa, dan majalisar ya ce ya shiga Kwankwasiyya tun yana da kudi, inda ya yi amfani da dukiyarsa wajen taimakawa tafiyar, kamar yadda ita ma ta taimaka masa wajen dawowa majalisar wakilai a 2023.
Ya ce, “Ko jam’iyyar NNPP kanta ta bayyana cewa a shirye take don yin tattaunawa da sauran jam’iyyu, don haka ba dole bane in bi hanyar jam’iyya. Ni dai na isa na dauki matsayar da na ga ta fi mini kyau.”
Sai dai ya ce duk da haka zai ci gaba da girmama Kwankwaso a matsayin jagoransa, ko da kuwa ba su kasance a jam’iyya daya ba.
“Ko da ban kasance tare da Kwankwaso ba, ba zan taba zagin shi ba, kamar yadda ban taba zagin Ganduje ba ko da mun rabu. Ban taba neman kwangila ba duk da cewa na taka rawa wajen nasarar NNPP a Kano. Kwankwasiyya ta tsaya min, amma ni ma na tsaya mata.”
Dan majalisar ya kara da zargin cewa babu wani babban dan siyasar arewa da ya taimaka masa lokacin da aka dakatar da shi daga majalisar wakilai a 2016, bayan ya zargi shugabannin majalisar da yin “Aringizo a kasafi.”
Lokacin da aka tambaye shi ko yana shirin barin NNPP, Jibrin ya ce, “Komai zai iya faruwa. Zan iya ci gaba da zama a NNPP, zan iya komawa APC, zan iya shiga ADC ko PDP ko ma PRP. Zan iya zuwa inda na ga dama. Duk lokacin da na yanke shawara, zan bayyana matsayina.”