Kakaki24 TV - Kakaki Online RTV

Kakaki24 TV - Kakaki Online RTV KAKAKI24 Gidan jarida ne na yanar gizo wanda ke kawo muku ingantattun shirye-shirye da Sahihan Labarai. Babban Ofis ɗin mu yana jihar Kano.
(1)

Domin Tallata hajarku ko kuma aiko da wani rahoto daga yankunanku sai ku tuntubemu ta watsapp a 09028244111.

Wannan shi ne sabon Page din Kakaki 24, a kansa za mu cigaba da wallafa labarai da sauran shirye-shirye. Sakamakon Ƴar m...
14/07/2025

Wannan shi ne sabon Page din Kakaki 24, a kansa za mu cigaba da wallafa labarai da sauran shirye-shirye. Sakamakon Ƴar matsala da wannan din ya samu.

Muna matuƙar godiya bisa ga yadda kuke bibiyarmu tare da ba mu shawarwari akan ayyukan mu.

https://www.facebook.com/share/p/19fSKoHzc7/

Muna yiwa ɗaukacin Mabiya KAKAKI24 Maraba da zuwa wannan sabon shafin.

Wancan shafin ya ɗan samu matsala ne hakan yasa muka ga dacewar mu buɗe sabo domin ci gaba da kawo muku Sahihan Labarai da kuma ingantattun shirye-shirye.

Muna godiya da bibiyar mu da kuke yi ba dare ba rana.

Allah ya bar zumunci.

Al'umma na ci gaba da cece-kuce kan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
14/07/2025

Al'umma na ci gaba da cece-kuce kan rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yan Bindiga Sun Tilasta Wa Ɗaruruwan Mutanen Mariga da Rijau a Jihar Niger Tserewa Daga Muhallinsu.Kakaki24 TV
14/07/2025

Yan Bindiga Sun Tilasta Wa Ɗaruruwan Mutanen Mariga da Rijau a Jihar Niger Tserewa Daga Muhallinsu.

Kakaki24 TV

"Muna Miƙa Ta'aziyyarmu ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari"- Narendra ModiFiraministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a sh...
14/07/2025

"Muna Miƙa Ta'aziyyarmu ga Nijeriya Bisa Rasuwar Buhari"- Narendra Modi

Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a shafinsa na X cewa ba zai manta da tattaunawar da s**a yi da marigayi Muhamamdu Buhari lokacin da ya ke kan mulki ba.

Ya kuma kara da cewa Buhari ya dukufa matuka wajen ganin kasashen biyu sun ci gaba da yaukaka dangantaka tsakaninsu.

A sakon nasa na ta'aziyya, Firaministan ya kuma ce da shi da Indiyawa biliyan 1.4 suna alhinin rasuwar Muhammadu Buhari.

Kakaki24 TV

14/07/2025

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana wasu muhimman wurare da take ganin ya kamata a mayar da hankali a kansu wajen sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya, A Gaban Kwamitin Gyaran tsarin mulkin kasar.

YANZU-YANZU: An dage jana'izar marigayi Muhammad Buhari sai zuwa gobe Talata 15 ga watan Yuli, 2025, da misalin karfe 2 ...
14/07/2025

YANZU-YANZU: An dage jana'izar marigayi Muhammad Buhari sai zuwa gobe Talata 15 ga watan Yuli, 2025, da misalin karfe 2 na rana a garin Daura, kamar yadda gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya shaida wa manema labarai jim kadan da isowarsa gida Nijeriya daga kasar Birtaniya.

Jami'an tsaro na kan shirye-shirye domin tarɓar gawar marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari a filin sauka...
14/07/2025

Jami'an tsaro na kan shirye-shirye domin tarɓar gawar marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari a filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa Yar'adua dake Jihar Katsina.

Sannan ana sa ran sanar da lokacin da za'a gudanar da Sallahr Janazarsa a mahaifar sa dake garin Daura ba da jimawa ba.

A madadin Madugun ɗariƙar Kwankwasiyya Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, da mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir ...
13/07/2025

A madadin Madugun ɗariƙar Kwankwasiyya Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, da mai girma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf. Hon Shehu M Bello (shehun Garu) yana miƙa saƙon ta'aziyya ga ɗaukacin al'ummar Najeriya bisa rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Allah ya jiƙansa yasa aljanna ce makomarsa. Ameen

Yanzu-Yanzu: An sassauto da tutocin Najeriya ƙasa, domin girmamawa ga marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
13/07/2025

Yanzu-Yanzu: An sassauto da tutocin Najeriya ƙasa, domin girmamawa ga marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Tinubu ya  Bukaci a Gaggauta Sauke tutocin Najeriya Kasa, Don Girmama Gawar Buhari.
13/07/2025

Shugaba Tinubu ya Bukaci a Gaggauta Sauke tutocin Najeriya Kasa, Don Girmama Gawar Buhari.

13/07/2025

"Kar ku zagi matattu..."! Haka Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama ya faɗa. Ku tsaftace harsunanku daga zagi ko aibata mutuncin matacce.

An Tura Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima London domin tahowa da gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ...
13/07/2025

An Tura Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima London domin tahowa da gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari gida Nijeriya.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kakaki24 TV - Kakaki Online RTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kakaki24 TV - Kakaki Online RTV:

Share