31/07/2026
Najeriya ta shiga wata haɗakar ƙasashe ƙarƙashin jagorancin Saudiyya domin kafa rundunar tsaro ta musamman da za ta kare zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Bab al-Mandab, bayan barazanar hare-haren mayaƙan Houthi da ke Yemen.
Sanarwar da Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta fitar ta bayyana cewa ƙasashe 14 ne s**a amince da shiga wannan haɗakar. Ƙasashen sun haɗa da Bahrain, Bangladesh, Djibouti, Masar, Jordan, Kuwait, Najeriya, Pakistan, Qatar, Somalia, Sudan, Turkiyya, Yemen da kuma Saudiyya.
Manufar rundunar ita ce tabbatar da tsaron Mashigar Bab al-Mandab da Tekun Bahar Maliya da kuma Tekun Gulf of Aden, domin kare jiragen ruwa da hanyoyin kasuwanci da makamashi daga hare-haren Houthi.
Matakin ya biyo bayan ƙarin barazanar da mayaƙan Houthi s**a yi ga jiragen ruwa masu alaƙa da Saudiyya, lamarin da ya ƙara dagula tsaro a yankin tare da haifar da fargabar tangarɗa ga kasuwancin duniya.