27/04/2024
Akwai abubuwan da ko da sun zo a karatu ba a ko'ina ya kamata a tattauna su ba, domin ko sahabbai irinsu AbaHuraira sun ɓoye wasu abubuwan da s**a sani a ilimance, domin gudun haifar da ruɗani da ɗaurewar kai.
Don haka, a wannan zamanin namu akwai karatuttukan da ba su aka fi buƙata ba, ya kamata a jingine su, ko k*ma a yi su ga ahalin abun. Domin yana daga cikin tozarta ilimi a yi magana da shi ba a muhallinsa ba. "Kowanne zance yana da muhallinsa"
Duk abun da za ka gaya wa mutane da sunan karatu indai zai sa su ji wani ƙaiƙayi a janibin Shugaba A.S to ba zai amfanar da su ba, sai dai ma ya cutar da su, ko uwa-uba ya halakar da su.
Babu abun da muka fi so irin mu ji ana ta faɗo mana martabobin Annabi A.S da ta maihaifansa da ahalin gidansa, amma duk abin da ya ci karo da wannan, babu abun da yake yi sai ƙona mana rai.
Mai Bulawus