16/07/2025
WATA SABUWA: Buhari Ya Saki Aisha Kafin Rasuwarsa - Inji Farfesa Farooq Kperogi
Shahararren ɗan jarida mai binciken kwakwaf ka Farfesa Farooq Kperogi ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya saki Matarsa A'isha Buhari kafin rasuwarsa.
"Jama’a na ta yaɗa wata magana da aka danganta ga Aisha Buhari, inda suke cewa Buhari ya nemi ta nemi gafarar ƴan Najeriya a madadinsa.
Ba zan iya tabbatar da ingancin wannan ikirari ba, amma abin da na sani shi ne kafin rasuwar Buhari, ba aure tsakanin shi da Aisha.
Sun rabu, Aisha ta komar da sunanta Aisha Halilu. Idan aka lura da kyau za aga Aisha ba ta je Daura ba a lokacin da ya yi ritaya bayan ya bar ofis. Buhari shi kaɗai ne daga baya ya koma Kaduna.
Hasali ma lokacin da ya kamu da rashin lafiya aka ce Aisha ta tafi Landan don ta kula da shi, sai aka ce ta hakura saboda ba matarsa ba ce. Bayan lallashi a ƙarshe ta tafi cikin ƴan kwanaki kafin ya mutu. Ko a yanzu, a wannan lokacin na jimami, akwai alamun saɓani.
Don haka ina matukar sha’awar sanin yaushe da kuma inda Buhari ya ce mata ta roki ‘yan Nijeriya a gafarta musa. A ina ma ta ce wannan?