23/05/2026
Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ana ƙara tambayar ko shugaban Amurka Donald Trump na rasa nasara a yaƙinsa da Iran ne duk da hare-haren farko da Amurka ta kai cikin watanni uku da s**a gabata.
Rahoton ya bayyana cewa Iran har yanzu na da tasiri a mashigar Hormuz tare da ci gaba da ƙin amincewa da wasu sharuɗan nukiliya duk da matsin lambar Amurka.
Masana harkokin siyasa sun ce Trump na fuskantar matsin lamba daga hauhawar farashin mai da raguwar farin jini a cikin gida yayin da rikicin ke ci gaba.
Sai dai Fadar White House ta ce Amurka ta cimma ko ta wuce dukkan manufofin sojinta a yaƙin da ta kira “Operation Epic Fury”.