28/05/2026
Matatar Dangote ta rage farashin dizal daga ₦1,800 zuwa ₦1,600 kan kowace lita yayin da ake samun ƙaruwar shigo da man fetur a Najeriya.
Rahoton TheCable ya bayyana cewa an aiwatar da rage farashin ne a ranar Talata 26 ga Mayu.
Jami’in hulɗa da jama’a na PETROAN, Joseph Obele, ya ce matakin na da alaƙa da ƙaruwar gasa a ɓangaren man fetur a ƙasar.
Ragin ya zo ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ke ci gaba da sauka.