07/01/2026
Kungiyar tsofaffin daliban ZAURA BABBA (ZOBA – Aji na 2008) ta gudanar da taron bankwana domin karrama tsofaffin shugabanninta, bayan kammala wa’adin mulkinsu.
A yayin taron, tsohon shugaban ƙungiyar, Ashiru Adamu Abdullahi, ya bayyana manyan ci gaban da ƙungiyar ta samu a tsawon shekaru goma da ya shafe yana shugabanci. Daga cikin nasarorin da ya ambata akwai ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ’yan ƙungiya, yin rijistar ƙungiyar bisa doka, da kuma gina allon bango na tile a cikin makarantar ZAURA BABBA, tare da wasu ayyukan alheri da s**a amfanar da makarantar.
Shi ma Principal na makarantar ZAURA BABBA, M. Idris Yau Ahmad, ya yabawa ƙungiyar bisa gudummawar da ta bayar, inda ya ce ayyukan da s**a yi sun dace kuma sun ƙara ɗaga martaba da darajar makarantar.
A nasa bangaren, Mataimakin Principal, M. Ashiru Usman Bello, ya bayyana cewa ƙungiyar ZOBA ta aji na 2008 ta bayar da gudummawa mai yawa, musamman gina allon bango na tile da kuma ziyarar da suke kaiwa makaranta domin jin matsalolinta. Ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin da za su karɓi ragamar jagoranci da su yi koyi da kyawawan ayyukan shugabannin da s**a gabata.