Tsaro Da Shari'a

Tsaro Da Shari'a Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tsaro Da Shari'a, News & Media Website, Kano.

Tsaro da Shari’a shafi ne na labarai da zai riƙa kawo muku sahihan rahotanni daga Najeriya da sauran ƙasashen duniya, musamman kan batutuwan tsaro, shari’a, laifuka, doka da sauran abubuwan da s**a shafi rayuwar al’umma.

Hukumar yaki da hana da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta k**a wasu nau’o’in kayan maye da a...
16/08/2026

Hukumar yaki da hana da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta k**a wasu nau’o’in kayan maye da ake zargin an shirya shigo da su jihar, bayan gano su a cikin wata motar bas.

Kakakin hukumar NDLEA reshen Kano, ASN Sadiq Muhd Maigatari, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Maigatari ya ce hukumar za ta fitar da cikakken bayani kan lamarin nan gaba.

Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta ce an kutsa cikin asusun X ɗinta, inda ta bayyana lamarin a matsayin matsalar tsaro ...
16/08/2026

Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta ce an kutsa cikin asusun X ɗinta, inda ta bayyana lamarin a matsayin matsalar tsaro ta yanar gizo.

Daraktan yada labaran tsaro, Samaila Uba, ya ce an dauki matakan kare asusun tare da kokarin dawo da cikakken iko a kansa.

Shelkwatar ta gargadi jama’a da su yi watsi da duk wani sako da ba shi da inganci daga asusun, tare da amfani da Facebook, Instagram da WhatsApp na hukumarta domin samun sahihan bayanai.

Al’ummar unguwar Gaida Kano sun yi zanga-zangar lumana kan satar yawaitar satar babura.Al’ummar unguwar Gaida, layin Aba...
16/08/2026

Al’ummar unguwar Gaida Kano sun yi zanga-zangar lumana kan satar yawaitar satar babura.

Al’ummar unguwar Gaida, layin Abacha Street, a karamar hukumar Kumbotso Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin neman kawo ƙarshen yawaitar satar babura a yankin.

Zanga-zangar ta biyo bayan k**a wani mutum mai suna, Mustafa Sani, da jami’an tsaron civil defense club reshen jihar Kano,NSCDC s**a yi, bisa zargin hannu wajen satar babura, inda s**a kwato babur guda ɗaya da lambobin babura 11 da sukudireba shida da makullan babura uku.

Al’ummar sun buƙaci hukumomin tsaro da Masarautar Kano su gudanar da cikakken bincike tare dau ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da hannu.

Mai unguwar Gaida Abacha Street, Alhaji Fatihu ya ce an kai masa rahotannin satar babura sama da 20 a yankin,Sai dai zargin bai zama hujjar aikata laifi ba har sai an tabbatar da shi ta hanyar bincike da doka. Inda al'amarin ke kara tayar musu da hankali.

Ya kuma ce abubuwan da jami’an s**a kwato na nuna irin girman matsalar da al’ummar ke fuskanta.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun kuma gabatar da zarge-zarge kan wani mutum mai suna Mansur S. Gaye, suna neman hukumomi su binciki zargin.

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kaddamar da bincike kan baturen yan asandan Jambutu, bisa zargin k**a jama’a ba bis...
16/08/2026

Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kaddamar da bincike kan baturen yan asandan Jambutu, bisa zargin k**a jama’a ba bisa ƙa’ida ba, tsare mutane ba tare da bin doka ba da kuma karɓar kuɗi kafin bayar da beli.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Matakin ya biyo bayan wani rahoto da ya yi zargin cewa wasu mazauna yankin Jambutu sun nemi a cire DPO ɗin daga muƙaminsa, bisa zargin aikata waɗannan laifuka.

Kwamishinan yan sandan Adamawa, CP Kabiru Umar Hassan, ya umarci mukaddashin mwamishinan yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka na Jiha (SCID), DCP Hamzat Tambai, da ya gudanar da cikakken bincike cikin sirri domin gano gaskiyar zarge-zargen.

Rundunar ta ce ba ta amince da k**a jama’a ba bisa ƙa’ida, tsarewa ba bisa doka ba, karɓar kuɗi ko wani nau’in rashin da’a daga jami’an ’yan sanda.

Haka kuma, ta jaddada cewa beli kyauta ne, kuma babu wani jami’in ɗan sanda da aka ba izinin karɓar kuɗi daga jama’a a matsayin sharadin bayar da beli.

16/08/2026

Yadda alumar unguwar Gaida layin Abacha Street, s**a fito domin gudanar zanga-zangar lumana don tsabtace unguwar daga batagarin sak**akon yadda Ake fuskanta sace-sacen babura.

16/08/2026

Yadda alumar unguwar Gaida layin Abacha Street, s**a fito domin gudanar zanga-zangar lumana don tsabtace unguwar daga batagarin sak**akon yadda Ake fuskanta sace-sacen babura

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsaro Da Shari'a posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share