
01/08/2025
Yanzu ko Har Abada: An Gaji da Wulaƙanci!
A Najeriya, nas-nas da ma’aikatan jinya su ne garkuwar lafiyar talaka. Su ne a tsaye dare da rana a asibitoci suna ceto rayukan mutane — amma me gwamnati ke saka musu da shi? Wulaƙanci, ƙasƙanci, da ko-in-kula!
Sai dai wannan karon, sun farka — kuma sun farka da murya DAYA! Sun fitar da wa’adin kwanaki 15 domin a gyara, ko kuma… a fuskanci fushinsu.
Dan Bello yace:
“Idan likita ya tafi ƙetare saboda rashin albashi mai kyau, kuma nas ke yajin aiki saboda wulaƙanci—waye zai ceci ran talaka? Gwamnati na wasa da lafiyar jama’a. Amma ran talaka ba katako ba ne.”