27/07/2025
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Hon. Bello Gambo Bichi yace
Ban fiye son rubutu a kafar sadarwa ta Facebook ba saboda girma dayazo mana. Amma ya zama lallai in mayar maka da martani bisa taba muhibbar jagororin jam'iyyarmu ta PDP da kayi wadanda s**a hanaka sakat kuma ka rasa tudun dafawa a cikinta domin anyi zaben shugabancin jam'iyyar baka sami koda dan sharar ofishiba a mazabar ka bare karamar hukumar ka ko jiha.
Munaso mu sanar maka Mai girma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Bello Hayatu Gwarzo kamar yadda kake yarfen sun zama ajojin Wike a wata kafar yada labarai, to Bara kaji:
1. Malam Ibrahim Shekarau ciwon hassada da kake masa da kiyayya inaso in tabbatar maka baya hudda da Wike amma akwai mutuntaka tsakaninsu domin inka tuna sunyi aiki tare da Wike a lokacin Malam Ibrahim Shekarau yana babban Ministan ilmi shi kuma Wike yana karamin minista, tun wannan lokacin basu sake wata mu'amala ba har kawowa yanzu. Kaidai kanaso ka bata shine da nuna shi makwadaicine, to yakamata kasan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Sardauna yasha gabanka. Yayi gwamna sau biyu a jiharka ta Kano yayi Ministan ilmi a tarayyar Nigeria sannan kuma ya wakilceka a majalisar dattawan Nigeria. Wanda jama'a nagartarsa s**a gani s**a zabeshi, kai kuma ka gaya mana sanda jama'a s**a taru s**a zabeka koda kansila ne.
2. Sanata Bello Hayatu Gwarzo, CON an zabeshi Sanata mai wakiltar Kano ta arewa har Karo hudu daga 1999 zuwa 2014, sannan kuma an zabeshi shugaban jam'iyyar PDP na arewa maso yammacin Nigeria. Yayi wakilci da gaskiya da rikon amana, ni nafi kowa sanin halinsa sakamakon aiki da mukayi dashi na wannan tsawon lokaci har kuma yanzu. Ba mutum bane mai kwadayi ko son abin duniya, shi har kullum duk abinda zai zubar da mutuncinsa baya ciki domin ba sarakene mai dattaku, kuma jiji da kansa na sarauta bazaisa ya zubar da mutuncinsa ba. Inaso in tabbatar maka da cewa bai taba gaisawa da Wike ba sai watarana a gidan Amb. Aminu Wali lokacin da yazo neman goyon bayan takarar Uche Secondus.