24/04/2026
An labarto cewa wannan mutumin dake wannan hoto sunan shi Ahmad Abdullah, ƙwararre ne a harkan magani dake aiki a wani wajen sayar da magani....
Kowani wata wata Dattijuwa takan zo gareshi domin sayan maganin ta. Zata tarar dashi akan teburin da ake biyan kuɗi, duk lokacin da ta ganshi, sai fuskar ta ta cika da annuri na farin ciki, shekaru kusan uku haka yake faruwa, idan dai tazo shi sai dai ya karɓi fam 200 na kuɗin Egypt ya Bata magani.
Ana nan sai wannan bawan Allah ya mutu, matar sai ta zagayo a ƙarshen wata kamar yadda ta saba, ta nemi maganin ta, taje teburin biyan kuɗin domin ta biya 200 kamar yadda ta saba.... Amma kuma sai bata same shi ba... Kafin ma ta buɗi baki ta tambayi Ina yake, sai sabon wanda ke karɓan kuɗi yace da ita: "Malama meye wannan wai?" Sai tace dashi: "kuɗin magani mana". Sai yace da ita: "Ae kuɗin ta 2000 ne ba 200 ba"
Cikin mamaki sai tace: "Amma sama da shekaru 3 haka nake saya 200 daga wajen wani matashi dake aiki anan kafin kai..... ko yana ina?"..
Sai sabon cashier yace da ita: "Allah ya mishi rasuwa"
Da aka duba cikin record sai aka tarar cewa wannan bawan Allah ya kasance yana cika mata 1800 daga cikin albashin shi a kowane wata
A yayin da mai shagon maganin ya gano hakan, shima sai ya yanke hukuncin kan cewa aci gaba da bata magani a wannan farashin a matsayin sadaqatuj jariya ga wanaan matashin da ya rasu..🥺
Ya Ubangiji Ka bamu zuciyar taimakon bayin ka, ka ƙara mana wadatar zuciya data aljihu albarkacin Muhammadur Rasoulullah sallallahu alaihi wasallam