24/09/2025
ANNABI NE FARKON KOMAI (saw)
Daga cikin dalilai da malamai suke dasu na gabatuwar Annabi (SAW) akan sauran halitta, akwai cewan Allah ya kafa dokar cewa duk wanda za'a bashi Annabta, dole sai ya yarda cewa zai zama mai imani da kuma taimakawa (k**ar sahabai) ga Annabi (SAW) idan ya zo musu.
Allah yana cewa;
KUMA KA AMBATA YAYINDA ALLAH YADAUKI ALQAWARIN ANNABAWA; INDA DUK NA BAKU LITTAFI DA HIKIMA SANNAN MANZO YAZO MUKU MAI GASKATA ABINDA KE TARE DAKU, ZAKU YO IMANI DASHI KUMA ZAKU TAIMAKESHI. YACE, SHIN KUN TABBATAR KUMA KUN DAUKARMIN ALQAWARI? SUNCE E! MUN TABBATAR. YACE, TO KU SHAIDA KUMA NIMA INA CIKIN MASU SHAIDA ¤ TO, DUK WANDA YA JUYA BAYA BAYAN WANNAN, TO WADANNAN SUNE FASIQAI"
___ A'li-Imrān (Qur'an 3:81)
Dan haka, ashe Annabi (saw) ya nan tun kafin Annabawa su sami Annabta; shine ma sharadin samun Annabtansu.