18/10/2025
TARON MATASA KAN BATUN TSARO
Kai Tsaye daga Dakin Coronation
Fadar Gwamnatin Jihar Kano
Ƙarƙashin Jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf
Ƙarfafa Matasa Don Gina Al’umma Mai Tsaro da Zaman Lafiya
RASHIN TSARO: Mu Wayar da Kai Kan Ta’addanci, Tashin Hankali da Sata
Rashin tsaro ya zama babbar barazana ga rayuwa da ci gaban al’umma. A kullum, muna fuskantar yawaitar ayyukan ta’addanci, tashin hankali da satar dukiyoyi da rayuka. Wannan matsala tana jefa jama’a cikin fargaba, tana hana ‘yan kasuwa gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, tare da hana matasa damar samun ci gaba a rayuwa.
Ta’addanci, ta’asa da sata ba su da wani amfani ga rayuwar al’umma. Suna haifar da rugujewar zaman lafiya, lalacewar dangantaka, da tabarbarewar tattalin arziki. Sata kuwa tana rushe amana, tana hana cigaba, tana haddasa talauci da zaman banza tsakanin matasa.
Wajibi ne mu fahimci cewa duk wanda ke shiga irin wadannan munanan ayyuka yana cutar da kansa da iyalinsa, tare da jefa al’umma cikin hatsari. Matasa, musamman, su gane cewa akwai hanyoyi na halal da za su bi don gina rayuwarsu da makomarsu ba tare da fadawa tarkon miyagun kungiyoyi ba.
Don haka, mu hada kai gaba daya:
Iyaye su zama masu kula da tarbiyyar 'ya'yansu.
Malamai da shugabanni su rika ba da ilimi da shawarwari masu gina zuciya.
Matasa su dage wajen neman ilimi da sana’a mai inganci.
Jama'a gaba daya su rika kai rahoton duk wata alama ta barazana ga tsaro.
Mu ci gaba da wayar da kan juna game da illolin aikata laifi, da kuma muhimmancin zaman lafiya da hadin kai.
Rashin Tsaro ba Matsalar Gwamnati Kadai ba Ce Matsalar Kowa Ce.