04/11/2025
Gwamnan Jihar Adamawa Ya Naɗa Sabon Shugaban Kwalejin Aikin Noma Ta Ganye
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da naɗin Aminu Kardu Tsigiya a matsayin sabonshugaba, Provost na Kwalejin Noma, Kimiyya da Fasaha ta Ganye, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Naɗin ya biyo bayan shawarar da Majalisar Gudanarwar Kwalejin ta bayar, bayan da Tsigiya ya fi kowa nasara a jarrabawar da aka gudanar don neman wannan muƙami.
Haka kuma, Gwamnan ya amince da naɗin Yusuf Haman Adama a matsayin Registrar na kwalejin, da Mustapha Baba Nasir a matsayin Librarian. Waɗannan naɗe-naɗe suna fara aiki nan take.
Yayin da yake taya sabbin shugabannin murna, Gwamna Fintiri ya buƙace su da su jagoranci cibiyar da hikima, gaskiya, da jajircewa, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa don ci gaban kwalejin.
Ya kuma umurci Provost ɗin da ya haɗa kai da sauran mambobin gudanarwa domin inganta ilimi da basirar aiki ga ɗalibai, tare da tabbatar da cewa kwalejin ta ci gaba da kasancewa cibiyar haɓaka harkar noma a jihar da ma wajen ta.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya shawarci sabbin shugabannin da su mayar da hankali kan ƙirƙire-ƙirƙire, bincike da hulɗa da al’umma, domin inganta martabar kwalejin da ci gaban jihar gaba ɗaya.