TNM News

TNM News TNM News (TrueNorth Media)

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Karɓi Baƙuncin Sanata Rufai Sani Hanga a AbujaA yau Juma’a, 17 ga Yulin 2026, Mai Girma Gwamn...
17/07/2026

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Karɓi Baƙuncin Sanata Rufai Sani Hanga a Abuja

A yau Juma’a, 17 ga Yulin 2026, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sanata Rufai Sani Hanga a ofishinsa da ke Abuja.

A yayin ziyarar, sun gudanar da tattaunawa mai amfani kan muhimman batutuwan da s**a shafi harkokin jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.

Sai dai, masu bibiyar harkokin siyasa na ci gaba da tambaya: Shin wannan ganawar tana da wata alaƙa da makomar siyasar Sanata Rufai Sani Hanga a gaba?

Kotun Koli Ta Tabbatar da Kwace Gidaje Bakwai, Dala Miliyan $2.045 da Takardun Hannun Jari na Godwin Emefiele ga Gwamnat...
17/07/2026

Kotun Koli Ta Tabbatar da Kwace Gidaje Bakwai, Dala Miliyan $2.045 da Takardun Hannun Jari na Godwin Emefiele ga Gwamnatin Tarayya

Kotun Koli ta Najeriya a ranar Juma'a, 17 ga Yuli, 2026, ta tabbatar da hukuncin ƙarshe na kwace wasu kadarori bakwai, kuɗaɗen dalar Amurka miliyan $2.045 da kuma takardun hannun jari da ake dangantawa da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, tare da mika su ga Gwamnatin Tarayya.

Alƙalan kotun guda biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Ibrahim Mohammed Saulawa sun yanke hukuncin bai ɗaya, inda s**a soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da dawo da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, wacce ta ce an samu hujjojin da ke nuna kadarorin na da alaƙa da kuɗaɗen da ake zargin an samo su ta haramtacciyar hanya.

Tun da farko, bayan Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin kwace kadarorin, Emefiele ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, wacce ta soke hukuncin.

Sai dai Hukumar EFCC ta garzaya Kotun Koli domin ƙalubalantar wannan hukunci.

Kotun Koli ta amince da ƙarar EFCC, tare da mayar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, wanda ya tabbatar da kwace kadarorin gaba ɗaya.

Kadarorin da aka kwace sun haɗa da gidaje da filaye a Lekki da Ikoyi na jihar Legas, wani katafaren ginin masana'antu da ake ginawa a Agbor, jihar Delta, da kuma wasu kadarori masu daraja.

Haka kuma kotun ta ba da umarnin a kwace kuɗaɗen dalar Amurka $2,045,000 da takardun hannun jarin Queensdorf Global Fund Limited tare da miƙa su ga Gwamnatin Tarayya.

Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari'ar, inda Kotun Koli ta tabbatar da cewa dukkan kadarorin za su ci gaba da kasancewa mallakin Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

16/07/2026

Manyan Daliban sheak muhammad sani yahya jingir,sun fara mummunar Addua wa Soja boy👇🏻

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ziyarci Sanata Rufai Hanga na jam’iyyar NDC tare da ƙoƙarin...
15/07/2026

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ziyarci Sanata Rufai Hanga na jam’iyyar NDC tare da ƙoƙarin shawo kansa ya koma jam’iyyar APC.

Ana cewa Sanata Rufai Hanga yana duba yiwuwar barin jam’iyyar NDC bayan ya rasa tikitin takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, da kuma damar zama mataimakin gwamna, sannan Rabiu Kwankwaso bai ba shi wani matsayi ba.

A jiya kuma, Hanga ya karɓi tawagar shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano da s**a kai masa ziyara a gidansa, yayin da ake ta rade-radin cewa ana tattaunawa kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

Yamai – Bayan wani samame da jami’an tsaro s**a kai, mahukunta sun rufe wata cibiyar tausa mai suna NINA MASSAGE & KINE,...
15/07/2026

Yamai – Bayan wani samame da jami’an tsaro s**a kai, mahukunta sun rufe wata cibiyar tausa mai suna NINA MASSAGE & KINE, bisa zargin gudanar da ayyukan da s**a saɓa wa doka.

Majiyoyin TNM News sun ce yayin binciken da aka gudanar a cibiyar, an gano wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan neman jinsi tsakanin mata.

Rahotanni sun nuna cewa an kwashe kayayyakin a matsayin hujjojin bincike, yayin da hukumomi ke ci gaba da tattara bayanai domin gano gaskiyar lamarin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa daga masu gudanar da cibiyar ba dangane da zarge-zargen da ake musu.

TNM News na ci gaba da bibiyar lamarin, kuma za ta kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu sabbin bayanai daga hukumomin da abin ya shafa.

EFCC Ta Kwace Jami’a, Gidan Rediyo Da Wasu Kadarori 46 Da Ake Alaƙanta Wa Da Abubakar MalamiHukumar Yaƙi da Yi Wa Tattal...
15/07/2026

EFCC Ta Kwace Jami’a, Gidan Rediyo Da Wasu Kadarori 46 Da Ake Alaƙanta Wa Da Abubakar Malami

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta samu nasarar samun umarnin kotu na kwace har abada kadarori 48 da ake alaƙanta wa da tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), zuwa hannun Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Hukuncin ya zo ne ranar Laraba, 15 ga Yuli, 2026, inda Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa EFCC ta tabbatar da cewa kadarorin na da alaƙa da kuɗaɗen da ake zargin an samu ta hanyar haramtattun ayyuka.

Daga cikin kadarorin da aka kwace akwai Rayhaan University da ke Jihar Kebbi, harabar jami’ar ta dindindin, ta wucin gadi, wani sabon shafi na jami’ar, gidan Mataimakin Shugaban Jami’ar, da kuma Rayhaan Radio da ke Birnin Kebbi.

Sauran kadarorin sun haɗa da manyan gidaje, otal-otal, shaguna, filaye da kadarorin kasuwanci da ke Abuja, Kano da Kebbi.

Haka kuma kotun ta kwace Rayhaan Agro Allied Factory tare da injuna da gine-ginenta, da kuma kadarorin Azbir Arena da s**a haɗa da otal, gidan buga takardu, masallaci, lambuna, Azbir Clothing da Azbir Pharmacy & Supermarket.

Daga cikin kadarorin akwai kuma Zeennoor Hotel da ke Kano mai ɗakuna 131, masallacin Zeennoor, gidan mai na Amasdul Oil and Gas Ltd., da wasu kadarori daban-daban.

A ranar 6 ga Janairu, 2026, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi bayan EFCC ta shigar da ƙara. Daga baya hukumar ta wallafa sanarwar a jaridu domin bai wa masu ruwa da tsaki damar bayyana dalilin da ya sa ba za a kwace kadarorin ba.

Abubakar Malami da wasu mutum 14 sun ƙalubalanci matakin, inda s**a nemi kotu ta soke umarnin kwace kadarorin tare da kalubalantar ikon kotun.

Sai dai kotun ta ce EFCC ta gabatar da isassun hujjoji, yayin da waɗanda ake ƙara s**a kasa nuna sahihin tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen mallakar kadarorin.

Kotun ta bayyana cewa a irin waɗannan shari’o’in kwace kadarori, ba ya isa mutum ya ce kadarorin nasa ne kawai; dole ne ya gabatar da hujjar cewa an same su ne ta hanyar halattattun hanyoyin samun kuɗi.

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shaidun ...
15/07/2026

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shaidun kariya a shari’ar da ake yi wa Umar Auwalu, Isyaku Yakubu da Yakubu Dayyabu, waɗanda ake tuhuma da kisan wata mata da ’ya’yanta shida a unguwar Ciranci da ke Kano.

Yayin da yake kare kansa a gaban kotu, Umar Auwalu ya shaida cewa shi kaɗai ne ya aikata kisan kanwar babansa da ’ya’yanta shida. Ya kuma yi ikirarin cewa wani boka mai suna Tomas ne ya ba shi wani turare tare da umartarsa ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka.

Umar ya ƙara da cewa Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu ba su da hannu a lamarin. A cewarsa, ya ambaci sunayensu ne bayan ya fuskanci wahalhalu a hannun ’yan sanda bayan k**a shi.

A zaman kotun na ranar, lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata sun gabatar da jami’in binciken ’yan sanda, Kofural Aliyu Jamilu, a matsayin shaida. Haka kuma, lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma sun gabatar da shaidun kariya domin kare waɗanda suke wakilta.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026.

Jami’an tsaro sun k**a wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙirar wata hukuma ta bogi da sunan Fad...
14/07/2026

Jami’an tsaro sun k**a wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙirar wata hukuma ta bogi da sunan Fadar Shugaban Ƙasa.

An bayyana cewa k**a Adeyemi ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar, sak**akon rashin halartar zaman shari’ar da ake masa.

Ana zargin mutumin da amfani da takardun bogi da kuma gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta kasancewar irin wannan hukuma, inda ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta taɓa kafa PFIPC ba, kuma ba ta naɗa Adeyemi a matsayin wani jami’in gwamnati ba.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026, yayin da Adeyemi ke fuskantar tuhume-tuhume guda takwas da s**a haɗa da zargin amfani da takardun bogi da kuma jabun hatiman gwamnati.

Idan aka tabbatar da waɗannan tuhume-tuhume a gaban kotu, zai iya fuskantar hukunci bisa tanadin dokokin ƙasar.

Mu muna fatan a yi sulhu, amma idan wani abin yake so a yi to sai a kawo shaidu, amma mu mun fi so a yi sulhu - Usman Ib...
11/07/2026

Mu muna fatan a yi sulhu, amma idan wani abin yake so a yi to sai a kawo shaidu, amma mu mun fi so a yi sulhu - Usman Ibrahim, Mijin wacce ake zargin Dr. Nisa’i da nema.

Matatar Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ta sanar da sake rage farashin fetur (PMS) da take sayarwa ga dillal...
03/07/2026

Matatar Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ta sanar da sake rage farashin fetur (PMS) da take sayarwa ga dillalai, karo na huɗu cikin wata guda, tana mai bayyana cewa za ta ci gaba da rage farashi idan farashin samar da man ya ci gaba da sauka.

A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar, ta ce ta rage farashin fetur da Naira 50 kan kowace lita, wanda ya sa jimillar raguwar farashin tun daga 30 ga Mayu, 2026 ta kai Naira 200 kan kowace lita. Hakan ya sa sabon farashin fetur daga matatar ya koma Naira 1,075 kan kowace lita.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa a wannan lokaci ya rage farashin man dizal (AGO) da Naira 300 kan kowace lita, yayin da ya rage farashin man jiragen sama (Jet A1) da Naira 520 kan kowace lita.

Dangote ya ce duk da cewa har yanzu yana tace ɗanyen man da aka saya a lokacin da farashinsa ya yi tsada a kasuwannin duniya, bai ɗora wa masu amfani cikakken nauyin ƙarin kuɗin ba. Maimakon haka, ya ɗauki wani ɓangare na asarar domin taimakawa wajen daidaita kasuwa, rage matsin tattalin arziƙi da kuma kare masu amfani daga tashin gwauron zabi na farashin mak**ashi.

Sanarwar ta ƙara da cewa farashin da matatar ke kayyadewa ba ya sauyawa kai tsaye da canjin farashin ɗanyen mai na yau da kullum a kasuwannin duniya, domin ana sayen ɗanyen mai ne makonni ko watanni kafin a tace shi, bisa yarjejeniyoyin kasuwanci.

Dangane da bayanan kamfanin, matsakaicin kuɗin da ya kashe wajen sayen ɗanyen mai da aka tace a watan Mayu ya kai dala 124.80 kan kowace ganga, yayin da a watan Yuni ya sauka zuwa dala 95.25 kan kowace ganga, idan aka kwatanta da farashin kasuwar duniya na kusan dala 71.01 kan kowace ganga.

Matatar ta ce yayin da take ci gaba da samun ɗanyen mai a ƙananan farashi, kuma tsofaffin hajojin da aka saya da tsada ke ƙarewa, akwai yiwuwar a ci gaba da samun raguwar farashin man fetur, muddin yanayin kasuwannin duniya ya ci gaba da kasancewa mai kyau.

Kamfanin ya jaddada cewa manufarsa ita ce samar wa ’yan Najeriya ingantattun kayayyakin mai a farashi mai sauƙi, tare da ƙarfafa tsaron mak**ashi, rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje, da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Address

Kano

Telephone

+2348106467597

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TNM News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to TNM News:

Shortcuts

Share