Voice Of Madungurum - VOM

Voice Of Madungurum - VOM Delight of people

19/05/2026

Vocab building

Idan mutum ya zauna kusa da kai ya matseka da Hausa ce wa mu ke "Ɗan matsa dan Allah" shi kam Bature ce wa yake "Give me some room".

Mr. Munib

TARIHINA BAZAI CIKA BA SAI DA MALAM !!A Yaune Za'ayi Addu'a Ta Shekara Daya Da Rasuwar Malaminmu Malam Ahmad (Yasayyadi)...
17/05/2026

TARIHINA BAZAI CIKA BA SAI DA MALAM !!

A Yaune Za'ayi Addu'a Ta Shekara Daya Da Rasuwar Malaminmu Malam Ahmad (Yasayyadi) Dan Asalin Unguwar Madungurun Mazaunin Gadar Salga Daga Baya Kuma Zuwa Kofar Waika, Jagoran Makarantar Hadiyyaturrahmaniyya Bayan Masallacin M. Ishaqa Rabiu Khalifa Allah Ya Jikansu Baki Daya.

Na Wuce Shekara Ashirin (20) Da Fara Karatu Wajen Malam Yasayyadi Karatu Da Ma'anar Karatu Wanda Aka Fi Sani Da Koyo Da Aiki, Malam Bai Koyamana Surutu Ba Bai Koyamana Alfahari Ba Bai Koya Mana Aminta Da Duniya Ba, Kuma Duk Wanda Ya Zauna A Gaban Malam Ya San Haka, Zaka Dade Baka Ga Irin Malam Ba Wani Mutum Mai Ban Mamaki Kuma Mai Boye Kai, Wata Ajiya Ce Ta Allah Da Take A Boye Da Yawa Basu Ganeta Ba Sai Bayan Fakuwarta.

Ina Rokon Adduoinku Ya Yan Uwana Ga Malaminmu Don Allah Wanda Ya Samu Iko Na Karanta Qulhuwa Gareshi Allah Ya Jikansa Ya Masa Rahma Ya Sanya Malam A Cikin Ceton Alqurani Ameen Rabb Ya Saka Malam A Cikin Diban Farko Na Ceton Shugabanmu Alaihissalam Allah Ya Kula Da Bayansa.

Abubakar Sunusi (Dan'umma)

Address

Dan'iya Street, Madungurum Quarter
Kano

Telephone

+2348140149105

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Voice Of Madungurum - VOM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share