PHARM.Gali Sule Media watch

PHARM.Gali Sule Media watch Director General Drug and Medical Consumables Supply Agency Kano state

09/07/2025
The DG DMCSA Pharm. Gali Sule has today, 8th July 2025, received donations of laptops, internet routers, and vehicles, i...
08/07/2025

The DG DMCSA Pharm. Gali Sule has today, 8th July 2025, received donations of laptops, internet routers, and vehicles, including delivery bans and mini buses from Capacity for Sustainable Development (C4SD) to boost last-mile delivery project.

The is an implementing partner and funded by the .


A yau Talata 8 ga watan Yuli, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA) P...
08/07/2025

A yau Talata 8 ga watan Yuli, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA) Pharmacist Gali Sule ya ziyarci garin Gaya inda ya yi wa iyalai da 'yan uwan marigayi Ubandoman Gaya Alh. Magaji Gaya gaisuwar ta'aziya bisa rasuwarsa.

Muna addu'a Allah Ya jikan sa, Ya gafarta masa.
PHARM.Gali Sule Media watch

A yau Talata ne 17 ga watan Disamba, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (D...
18/12/2024

A yau Talata ne 17 ga watan Disamba, Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano (DMCSA), Famasist Pharm Ghali Sule Fpsn ya halarci taron kafa harsashin gina kamfanin yin magunguna a birnin Ikko.

Sabon kamfanin da aka kaddamar da gininsa a yau mallakin kamfanin magunguna ne na Jawa International Ltd.

A lokacin ziyarar, Famasist Gali Sule yana tare da Daraktan Samar da Magunguna na hukumar DMCSA Famasist Tukur Ibrahim.
✍️ PHARM.Gali Sule Media watch
17/12/2024

Sanarwar Manema LabaraiDMCSA Ta Lashe Lambobin Yabo a Taron Masu-Ruwa-da-Tsaki Na KasaAn karrama Hukumar Samar da Magung...
13/12/2024

Sanarwar Manema Labarai

DMCSA Ta Lashe Lambobin Yabo a Taron Masu-Ruwa-da-Tsaki Na Kasa

An karrama Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta jihar Kano (DMCSA) a wajen Taron Shekara-shekara na Masu-Ruwa-da-Tsaki a Kan Samar da Magunguna na kasa wanda ya gudana a jihar Legas.

Hukumar Samar da Magungunan ta Jihar Kano ta samu lambobin yabo har guda biyar (5) sakamakon aiki tukuru da jajircewar shugabanninta.

Da yake kar6ar lambobin yabon, Darakta-Janar na Hukumar, Famasist Gali Sule ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon goyon baya da hadin kai da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake bai wa hukumar karkashin kulawar Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano.

Ya kara da cewa ma'aikatar tasa ta yiwa takwarorinta na sauran jihohi fintinkau sakamakon kyawawa da kuma managartan manufofi da tsare-tsaren inganta harkar lafiya da gwamnatin jihar nan karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta 6ullo da su.

Famasist Pharm Ghali Sule Fpsn ya jadadda kudirin gwamnati na samar da wadatattu kuma ingantattun magunguna masu rahusa a dukkanin asibitocin da ke fadin jihar nan.

Taron da aka shafe kwana uku (3) ana gudanarwa ya samu halartar jami'an daga hukumomin samar da magunguna na jihohi, kamfanonin yin magunguna, hukumomin masu ba da lasisin samar da magunguna,, cibiyoyin bincike, da kuma kungoyin tallafawa kasashe masu tasowa.

Sanarwa
PHARM.Gali Sule Media watch
A.I YARO MEDIA GROUP
13/12/2024

03/12/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdullahi Ghali, Rangaza Portrait

DG Pharm Ghali Sule Fpsn a yau 28 ga watan Nuwamba ya karbi bakuncin  shugabanin kungiyar Young Pharmacists Group (YPG) ...
28/11/2024

DG Pharm Ghali Sule Fpsn a yau 28 ga watan Nuwamba ya karbi bakuncin shugabanin kungiyar Young Pharmacists Group (YPG) ta jihar Kano karkashin jagorancin Shugabar kungiyar Famasist Salma Adamu Dangwani,.wadanda s**a kai masa ziyarar ban-girma a ofishinsa.

Sauran mambobin tawagar YPG sun hada da Famasist. Mustapha Sulaiman Sakataren Kudi da kuma Famasist Aminu Usman Shanono Sakataren kungiyar.
PHARM.Gali Sule Media watch

The DG DMCSA Pharm Ghali Sule Fpsn has attended the _State Taskforce Committee on Immunization Meeting_ currently going ...
28/11/2024

The DG DMCSA Pharm Ghali Sule Fpsn has attended the _State Taskforce Committee on Immunization Meeting_ currently going on at Africa House, Government House, Kano, and chaired by Deputy Governor Cmrd. Aminu Abdussalam Gwarzo.
✍️ PHARM.Gali Sule Media watch

*DG Pharm. Gali Sule da hukumar DMCSA* a yau 26 ga watan Nuwamba sun karbi bakuncin *KHETFUND Assessment Team* wanda *Ex...
27/11/2024

*DG Pharm. Gali Sule da hukumar DMCSA* a yau 26 ga watan Nuwamba sun karbi bakuncin *KHETFUND Assessment Team* wanda *Executive Secretary Dr. Fatima Zahraddeen* ta jagoranta. Tawagar, wacce ta kunshi ma'aikata daga MDAs masu dacewa, sun kai ziyarar ne don duba sabon ginin da aka gina PharmaGrade Warehouse da Sashin Masana'antar Magunguna (DMU) a matsayin wani bangare na ayyukan KHETFUND a DMCSA.
PHARM.Gali Sule Media watch

28/08/2024
*Pharm. Gali Sule Commissions ofishin Kwankwasiyya dake Gombe, ya hada da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar*Shugaban Kwami...
24/08/2024

*Pharm. Gali Sule Commissions ofishin Kwankwasiyya dake Gombe, ya hada da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar*

Shugaban Kwamitin Tuntubar Shugaban Kwankwasiyya na Kwankwasiyya ya kaddamar da ofishin Kwankwasiyya a Jihar Gombe, Laraba.

Da yake jawabi yayin kaddamar da ginin, Shugaban NNPP na jihar Gombe Hon. (Dr.) Rambi Ibrahim Ayala ya ce kungiyar Kwankwasiyya ta samu gindin zama a jihar, inda ya ce tafiyar tana da tsari tun daga matakin Unguwa, Kananan Hukumomi, da Jiha.

Pharm Ghali Sule Fpsn, wanda kuma shine Darakta-Janar na Hukumar Samar da Magunguna da Magunguna ta Jihar Kano (DMCSA), ya yabawa Hon. Adamu Muhammad Gargajila wanda ya bada gudumawar ginin, goyon baya da jajircewa ga tafiyar Kwankwasiyya.

A rangadin na kwanaki 3, wanda ya fara daga ranar Laraba 21 ga wata zuwa Juma’a, 23 ga watan Agusta, kwamitin ya samu kwarin guiwa da tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Shugaban kwamitin ya samu rakiyar Hon. Abubakar Sadik Kibiya, SSA ga Gwamnan Jihar Kano; Hon. Yusuf Ali Maigado dan majalisa mai wakiltar Tsanyawa/Ghari a majalisar jiha, Hon. Zangina Jafaru da Garba Abdu Roller.

Sauran su ne Hon. Kabiru Gombe, Tasiu Adam Hotoro, Hon. Abdullahi AM Wali, da Hon. Abdulrazak Ibrahim Yaro, Mataimaki na Musamman ga DG.

*PHARM GALI SULE MEDIA WATCH*

31/07/2024

Shi ma Shugaban kamfanin magunguna na ASAD Pharmaceuticals Ltd. Dakta Shehu Ya'u Sa'ad ya ziyarci Pharm. Gali Sule don yi masa ta'aziya a yau Asabar 27 ga watan Yuli.

Address

Dawakin Dakata
Kano

Telephone

+2349162714470

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PHARM.Gali Sule Media watch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to PHARM.Gali Sule Media watch:

Share