06/09/2026
ENGR. ABBA KABIR YUSUF YA KADDAMAR DA OFISHIN NORTHWEST TINUBU SUPPORT GROUP A KANO
Bayan kammala babban taron Ƙaddamar da Shugabancin Tinubu Support Group na Ƙasa, wanda aka gudanar a Jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, tare da ɗimbin manyan baki da masu ruwa da tsaki, ya jagoranci ƙaddamar da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR na Tinubu Support Group na Arewa maso Yamma, wanda ke Kano tare da Ƙaddamar motocin yaken neman zaben TSG
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Prof. Nentawe Yilwatda da tsohon shugaban Jam'iyyar APC na kasa, tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Patron na Tinubu Support Group, Rt. Hon. James Abiodun Faleke da Sanatocin Jihar Kano guda uku; Ministoci; ’Yan Majalisar Dokokin Jiha da ta Tarayya; da sauran manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki na daga cikin mahalarta
Ƙaddamar da wannan ofishi na daga cikin muhimman matakai wajen ƙarfafa tsari, haɗin kai da shirye-shiryen Tinubu Support Group a yankin Arewa maso Yamma, domin tallafa wa tafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR a babban zaɓen 2027.
Hon. Nasiru Usman Naibawa (Zico)
SLA ga Shugaban Majalisar Dattijai.
By SAYYADI HARUNA. KUTAMA
(VOA)