01/08/2025
MAZA GUMBAR DUTSE: Yadda Marigayi Janar Muhammadu Buhari Ya Fatattaki Sòjòjìn Chadi Haŕ Ya Antaya Cikin Kasarsu
A 1980s, lokacin da Alhaji Shehu Shagari ke mulki, sojojin kasar Chadi s**a mamaye wani yanki na ƙasar Nìjeriya dake kan iyaka.
Shagari ya bada umarni ga Kwamandan Rundunar Arewa maso Gabas a lokacin, Janar Muhammadu Buhari, da ya tunkari wannan barazana. A cikin kankanin lokaci, Buhari ya jagoranci dakarunsa zuwa bakin iyaka domin a fafata, Buhari ya fatattaki sojojin Chadi, kuma ya kore su da karfi da yaji.
Amma Buhari bai tsaya a kan iyakar Nijeriya ba, sai da ya bi su har cikin ƙasar Chadi domin ya tabbatar da cewa sun fahimci cewa Nìjeriya ba kanwar lasa ba ce, kuma kada su kuskura su sake irin wannan kuskuren.
Yayin da yake ci gaba da shikar su, sai shugaban kasa Shagari ya aiko masa da umarnin ya dakata kuma ya dawo gida saboda ya fahimce Janar Buhari na kokarin ya wuce gona da iri. Wannan umurni bai yi wa Buhari daɗi ba. A matsayin sa na soja, ya yi imani da cewa aikin da aka ba shi bai kammala ba.
Wannan lamari ya nuna jarumtar Buhari da kwarewarsa a fagen yaƙi. Wasu ma na ganin cewa wannan umurni da Shagari ya bawa Janar Buhari da ya dawo gida na cikin dalilan da ya sa Buhari ya yi wa Shagari juyin mulki.
Daga Mukhtar Yusuf