Hausa News

Hausa News Labarun Hausa

A ganinku, wace hanya ya kamata gwamnati ta bi wajen yaƙi da ta'addanci?
11/08/2025

A ganinku, wace hanya ya kamata gwamnati ta bi wajen yaƙi da ta'addanci?

إِنَّمَا يُعْرَفُ الإِخْلَاصُ عِنْدَ الشِّدَّةِ وَالتَّضْحِيَة' Ana fahimtar (me) tsantseni ne lokacin tsanani da kuma l...
03/06/2025

إِنَّمَا يُعْرَفُ الإِخْلَاصُ عِنْدَ الشِّدَّةِ وَالتَّضْحِيَة

' Ana fahimtar (me) tsantseni ne lokacin tsanani da kuma lokacin sadaukarwa'- inji Larabawa

Tsananin rayuwa da lissafin ta a rayuwar da muka tsinci kan mu ciki ya sa da dama daga cikin mu ba su iya alheri (ciyarwa, sadaka, kyauta, ko wasu ayyukan Ibadah manya kamar aikin Hajji da layya).

Amma a zahirin gaskiya, ɗan Adam ba zai taɓa wadatuwa da abin duniya (kuɗi) ba har ya koma ga Allah maɗaukakin Sarki. Idan a baya kafin a yi ƙarin albashi, kana kallon Naira dubu saba'in (70,000) a matsayin babban kuɗi, shin har yanzu da kake samun ta kowane wata, kana kallon darajar ta?

Da yawan mutanen mu su kan ce da a biya musu kuɗin kujerar Hajji gwara a ba su kuɗin ko rabin sa su kashe damuwar gaban su. Hakan ya sa su da sauƙe farali sai dai su ji labari.

Idan ka ƙi sayen ragon layya a wannan shekara saboda kana da buƙatu da za ka yi da kuɗin, to wata shekarar (idan ma ka gan ta) za ta zo da irin na ta buƙatun, wata ma haka, ta gaban ta ma haka.

Dole sai mun daure zukatan mu don gudanar da wasu ayyukan Ibadah da kuma kyautatawa, idan ba haka ba to za ka iya wata guda cif ba ka taimaki wani me tsananin buƙata ba.

Wani malami yana cewa:
لا مَجْدَ بِلَا تَضْحِيَة، وَلَا تَضْحِيَةَ بِلَا مِحْنَ

"Babu ɗaukaka (girma) ba tare da sadaukarwa ba, kuma babu sadaukarwa ba tare da wahala (kewar abinda aka kyautar ba).

Yana daga cikin tsantsar imani da Allah yarda da cewa Shi ne me bayarwa kuma Ya karɓa. Sannan kuma sadaukarwa cikin ayyukan bautar Allah ba ta jawo talauci.

Allah ya ba mu ikon sauƙe farali. Amin.

Salmanu Isah Darazo
Yuni 3, 2025.

Address

No 30/31 Gadangami Complex. Kabuga
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa News:

Share