29/04/2026
AURAN GATA
ANGO DA AMARYA (3000)
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf za ta gudanar da wani shiri na musamman na aurar da zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wato maza 1,500 da mata 1,500.
Wannan shiri ya fi karkata ne ga marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu rayuwa mai inganci ta hanyar aure.
Abubuwan da aka tanada ga ma’auratan sun haɗa da:
1. Kayan ɗaki: gado, sif, madubi, katifa, filo da zanin gado.
2. Kayan abinci: shinkafa, taliya, da man girki.
3. Kayan sawa ga mata: atamfa da hijabi.
4. Kayan sawa ga maza: shadda da hula.
5. Sadaki: Naira dubu ɗari (₦100,000).
6. Jari ga mata: Naira dubu ɗari (₦100,000) domin fara sana’a.
Haka kuma, za a gudanar da gwajin lafiya tare da cike takardun (forms) guda uku domin tabbatar da cewa duk wanda zai shiga shirin ya cika dukkan sharudda.
Ƙarin bayani
(Duk wanda zai shiga wannan shiri sai yana da sanaa.)
Allah ya saka wa gwamna da alkhairi, ya sanya wannan aiki ya zama alheri mai ɗorewa ga al’umma, ya kuma sa ya zama sanadin rage talauci da inganta zaman lafiya a jihar Kano.