14/09/2025
Daren Farko
Bayan an yi shagalin bikina da amaryata, an kawo ta dakinta cikin annashuwa.
Tun kafin dare ya yi sosai na matsa wa abokaina su raka ni dakin amarya, muka tafi cike da raha da zolaya.
Da muka shiga, amaryata ta sha ado da kwalliya, tana ta sheƙin kamshi. Hannunta na ɗauke da lalle abin sha’awa. Na ce:
“Amarya, bake laifi”
Ta yi murmushi mai ɗaukar rai, cikin siririyar murya tace:
“Angona, ka sha kamshi.”
Bayan gajeriyar hirar soyayya, na ce:
“Yakamata mu yi alwala, mu yi nafila, mu dabbaka Sunnah.”
Ta dubeni da murmushi tace:
“To, amma ka manta wata Sunnah.”
Nan da nan na tuna min kamar yadda manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya koyar: a daura hannu kan amarya a yi addu’a. Sai na ce da murmushi:
“Kai, wannan shi ne dadin auren mace mai ilimi.”
Mun yi sallah, sannan na ce:
“Cutie pie, ki ci abinci. Ga kazarki ta musamman da soft drinks.”
Amaryata ta ce:
“A’a honey pie, na koshi.”
Sai na dage:
“Ai ba haka ba ne. Ga Peak Milk mai sanyi, ga Maltina, ga Paro. Ki sha mana.”
Ta yi dariya ta ce:
“To, amma kai ka fasa min angona.”
Na ɗauko kofi na fasa mata, na yi mix, na bata a baki ta sha. Itama ta bani in sha. Daga baya ma sai da na ɗiba kazar da na siyo ina bata a baki kamar jaririya.
Da muka kammala, sai na ce:
“Cutie pie, yanzu lokaci ya yi. Ki tashi ki sa kayan bacci, ki kwanta ki samu nutsuwa.”
Ta kalle ni, ta yi murmushi:
“Kai fa?”
Na ce:
“Ni zan yi shafa’i da wuturi kafin.”
Da na gama sallah na juyo, sai na ganta ta canza kaya, ta yi wani dressing mai ban sha’awa tana kwance a kan gado. Na tsaya cak ina kallonta, sai na ce:
“Cutie pie, wannan irin dressing din fa ba zai bari in yi bacci ba.”
Ta murmusa ta ce:
“Ai kai ne kace nayi. Ni kuma ba zan iya sabawa mijina ba tun a darenmu na farko.”
Na ce:
“To yanzu ya za’ayi kenan?”
Ta ce:
“Kawai kai ma kayi dressing, mu yi abin da zai kawo farin ciki.”
Nan na kashe fitila, na hau kan gado kusa da ita. Da zan daura hannu kanta kawai sai na ji an taba ni a baya:
“Katashi kayi sallar Asuba!”
Na juya da mamaki — ashe mafarki nake yi, abokina Abubakar El-serdique ne ke tsaye akaina yana tashi na wai ashe mun makara.
Sai na dafe kai nace:
“Allah ka aurar da mu gaba ɗaya.”