
12/05/2025
KAƊAN DAGA CIKIN HUƊUBAN DA SHEHU RTA YAYI LOKACIN TARON "MIHRAJAN" (CELEBRATION) NA ƊALUBAN ISLAMIYYA A KAOLACK DA YAMMACIN RANAR LAHADI SHAƊAYA GA WATAN RABI'UL AUWAL.
Ya bayyana aƙidan musulunci kaɗai bazai isa ba, dole sai an nemi ilimi da kuma aiki dashi. Dole sai anyi juriya da yin Jihadi (ƙarami da Babba) da rashin tauye lokaci daga cikin lokuta da hali daga cikin halaye. Da barin waswasi da zace-zace (kokonto), da al'adu masu cutarwa, da saɓon Allah da bin sawun sheɗan.
Babu makawa; dole sai an dawwamar da juriya, Juriya cikin massala umarce-umarcen Allah da juriya wajen gujewa hane-hanensa......
Ƴan uwa; Musulunci yanda Qur'ani ya bayyana mana shine: imani da Allah shi kaɗai, da imani da Annabi (SAW), sannan ƴan'uwantaka da daidaito, da haɗin kai, da taimakon juna, da jin ƙan juna. Ba yanke zumunci, babu faɗa, babu fushi da juna, babu Hassada. Kowani mutum musulmi yanada cikakken ƴanci da zai yi aiki dan duniyar sa dakuma lahirarsa. Ga musulmi Yakamata yayi aiki da zai amfani kansa dakuma al'umma gaba ɗaya. "Fiyayyen mutane shine wanda yake amfanar da mutane"......
Duk wanda yabar aiki yana jefa samuwarsa ne cikin halaka yau dakuma gobensa, dan haka nake faɗa; ina ganin cewa rayuwa itace aiki. Duk wanda yayi kasala ga barin aiki toh zai zama mai buƙatuwa zuwa ga waninsa. "Hanun dake bayarwa, yafi hannun dake ƙarba". Dole ne sai anyi aiki domin abinda rayuwa zataci yau da kullum, da kuma ruhi. Karkata gaba ɗaya zuwa abinda rai zataci yau da kullum batare da waiwaya zuwa ga ruhi ba yana rusa izza, ƙarfi, da kuma jiki....
Domin musulmi izzarsa yana cikin riƙo da ilimin addini (islamiyya) a nan ƙarfinsa yake, wahalarsa kuwa yana a cikin barinsa da Addini. Hanyar komawa zuwaga izza da kuma ƙarfi shine: komawa ga aiki da ilimin addini.....
Mamaki ga musulmi; ya kasance yana bin Alqur'ani amma baya aiki dashi.....
Dukkanin cuta yana cikin jahilci, maganin sa kuwa shine komawa ga ilimi, ginin maƙiya addini yayi stayi shekara ɗari cikin zarema musulmai ilim