Jama'atu Media Kano

Jama'atu Media Kano Don ilimantuwa da nishadi cikin lamarin Annabi SAW

•GA MALINTA GA KWALLIYA GA KUƊI SANNAN GA NASABA DA MANZON ALLAHﷺ Shugaban Kungiyar Jama'atu Ahbabu Rasulullahiﷺ Associa...
03/10/2026

•GA MALINTA GA KWALLIYA GA KUƊI SANNAN GA NASABA DA MANZON ALLAHﷺ

Shugaban Kungiyar Jama'atu Ahbabu Rasulullahiﷺ Association Of Nigeria Kenan, Wato Sheikh Sharif Sani Janbulo Cikin Shiga Ta Alfarma Yayin Gabatar Da Mauludi ANNABIﷺ Mai Taken Ayyamul Muhammadiyya Na Wannan Shekarar Ta 1448/2026.

Wanda Yasaba Shiryawa Duk Shekara A Ranakun 16 Da 17 Dakuma 18 Gawatan Rabbi'ul Auwal, A Gidan sa Dake Unguwar Kabuga Janbulo First Gate A Birnin Kano, Wannan Shiga Itace Ta Ranar Farko, Muna Addu'ar Allah Yamaimaita Mana Alfarmar ANNABIﷺ

📸LABARAN PHOTOGRAPHY

JAMA’ATU AHBABU RASULULLAH ke sanar da ku jadawlin majalisan da Sheikh Sharif Sani Janbulo zai gabatar a wannan satin in...
03/10/2026

JAMA’ATU AHBABU RASULULLAH
ke sanar da ku jadawlin majalisan da Sheikh Sharif Sani Janbulo zai gabatar a wannan satin inshaAllah

1. Asabar 3/10/2026 Rijiyar Zaki 9:00pm
2. Lahadi 4/10/2026 Babawa Mauludin Abba sojan Sidi 9:00pm
3. Litinin 5/10/2026 Kabo 9:00pm
4. Alhamis 8/10/2026 Dan rimi 9:00pm
5. Juma’a 9/10/2026 Birgade 9:00pm
6. Asabar 10/10/2026 Kwana Hudu 9:00pm

Duka zaku iya kallon Live na jawabin da Malam zai gabatar a shafin sa da ke facebook mai suna “Sharif Sani Janbulo”

•LALLAI ANNABI ANNABI: Aduk lokacinda na tuna girma da Kuma matsayin Annabi saina ji zuciya ta tacika da farin ciki mara...
02/10/2026

•LALLAI ANNABI ANNABI: Aduk lokacinda na tuna girma da Kuma matsayin Annabi saina ji zuciya ta tacika da farin ciki maras musaltuwa, sannan Kuma sainaji soyayyar Annabi t takara mamayemin zuciya ta Kuma saina Kara godewa Allah, Daya bamu Annabi Muhammad saw, Kuma yayomu cikin masoya Annabi wannan bakaramar karramawa bace daga gurin ubangiji SWA.

Muyi sani cewa babu Wanda zamuyi ladabi dakuma makauniyar soyayya kamar Annabi saw, Domin idan muka duba shine Wanda Allah yake ta shela Acikin Alqur Ani Mai girma surori daban daban suna magana Akan matsayin Annabi, gakuma Annabawa suna ta yin shela Akan idan Annabi yazo yazo to Abar shariasu Azo Abi tashi domin dama sudin yaransane, domin naji Allah yana kafa musu sharadi Akan idan sunzo zasu tayashi Aiki sukace sun Amince zasuyi Hakan, duk sanin masana sunyi sun gaji domin babu Wanda yasan Annabi Koda sakan idan ba sarki Allah ba.

Anas Na Annabi
07018916555

© Head bloggers Department Jamaatu media Kano state

•RIJIYAR ZAKI: Insha Allahu Ranar Asabar Mai Zuwa 3/10/2026, Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo Zai Gabatar Da Majalasi ...
01/10/2026

•RIJIYAR ZAKI: Insha Allahu Ranar Asabar Mai Zuwa 3/10/2026, Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo Zai Gabatar Da Majalasi A Unguwar Rijiyar Zaki A Jihar Kano.

Baba Sidi Zai Gabatar Da Majalasin A Makarantar MU'ASSATUL WUDADUN NABIYﷺ Wadda Take A Unguwar Rijiyar Zaki, Daura da Gidan Man AAS Marmaro, Bayan Gidan Mallam Nasiru Hamisu.

Lokaci: Da Misalin Karfe 9 Na Dare Insha Allahu, Allah Yabada Ikon Zuwa Amin Summa Amin.

InshaAllah gobe Juma’a Imamul Ahbabu Rasulullah Sheikh Sharif Sani Janbulo zai dawo gabatar karatun Umdatul Ahkam wanda ...
01/10/2026



InshaAllah gobe Juma’a Imamul Ahbabu Rasulullah Sheikh Sharif Sani Janbulo zai dawo gabatar karatun Umdatul Ahkam wanda aka saba yi duk Juma’a a gidan sa da ke janbulo first gate da misalin karfe 6:00 na yamma.

Duka zamu haska muku live a shafin Sheikh Sharif Sani Janbulo da ke Facebook inshaAllah.

✍️Jama'atu Media Kano

29/09/2026

• DAIMAN SAI ANNABI

•Daga Wajen Taron Mauludin ANNABIﷺ Awannan Ta Litinin 28/9/2026, Wanda Ake Gabatarwa A Garin Dan kwali Yankin Karamar Hu...
29/09/2026

•Daga Wajen Taron Mauludin ANNABIﷺ Awannan Ta Litinin 28/9/2026, Wanda Ake Gabatarwa A Garin Dan kwali Yankin Karamar Hukumar Gezawa Jihar Kano.

Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo Yasamu Shigowa Filin Taron, Allah Yasa Agama Lafiya Alfarmar ANNABIﷺ

• DARAJOJI UKU:1» Mafi Girman Allah Kaɗai Ya San Ta2» Ta Tsakiyar Allah Da Annabi ﷺ Kadai S**a San Ta3» Karamar Ce Saura...
28/09/2026

• DARAJOJI UKU:
1» Mafi Girman Allah Kaɗai Ya San Ta
2» Ta Tsakiyar Allah Da Annabi ﷺ Kadai S**a San Ta
3» Karamar Ce Sauran Mutane Aljannu, Malā'iku Da Dukkan Tālikai Muka Sani.

Duk Wannan Kai-Kawo Da Ake Tsakanin Masu Yabo, Kowa Yana Faɗar Darajar Annabi ﷺ Iyākar Ƙoƙarin Sa Babu Wanda Zai Iya Faɗar Ɗigo Na Darajar Annabi ﷺ A Iya Wacce Allah Ya Sanar Da Tālikai Ɗin Ma.. To Ya Kake Tunanin Za'a Ƙetare Ta Har A Kai Ga Darajar Da Annabi ﷺ Kaɗai Ya Sani B***e A Tsallaka Zuwa Ga Wacce Ba Wanda Ya San Ta Sai Allah?

Ya Kai Mai Yabo; Ka Yi Iya Yanda Zaka Iya Yi Na Yabon Annabi ﷺ Ka Zuba Irin Ka Iyā Ƙarewar Sa, Gonar Annabi ﷺ Bata Da Ƙarshe B***e A Wuce Ta Da Iri. Amma Ka Riƙi Nasīha Biyu Daga Manyan Masu Yabon Annabi ﷺ Guda Biyu

1.IMĀMUL BŪSĪRY; Ka Bar Abin Da Nasara S**a Yi Da'awar Sa Cikin Annabin Su (Ma'ana Kar Ka Kira Shi Allah, Ko Ɗan Allah) Amma Ka Yi Hukunci Da Abin Da Ka So Yayin Da Kake Yabon Annabi ﷺ, Kuma Ka Kyautata. Ka Jingina Duk Abin Da Ka So Na Ɗaukaka Zuwa Ga Zātin Sa, Haka Nan Ka Danganta Duk Abin Da Ka So Na Girma Zuwa Ga Alƙadarin Sa. Domin Haƙiƙa Falalar Manzon Allah ﷺ Bata Da Iyāka B***e Mai Furuci Da Baki Ya Iya Yin Bayanin Ta Baki Ɗaya!

2» GAUSUZ-ZAMĀN NIASSE; Idan Har Ka Ce Annabi ﷺ Bawan Allah Ne (Baka Kira Shi Allah Ko Ɗan Allah Ba) Sannan Shugaban Halittun Allah, To Kai Faɗi Duk Wani Abin Da Ka So Na Yabo A Cikin Shi, Kar Ka Wani Ji Tsoron Kāfirci. Domin Shi Ne Duka, Kuma Duka Daga Gareshi Ne Wannan Haka Yake, Kai, Haƙiƙa Shi Ubangijin Shi Ne Ya Zaɓe Shi Kuma Ya Bashi Tun Tuni, Babu Wani Hanawa!

Da Wannan Nake Taya Ƴan Ansāru Murnar ZAGAYOWAR Ranar Zagayen Maulidin Annabi ﷺ Na Islāmiyyu A Yau. Allah Ya Tashe Mu Lafiya Cikin Soyayyar Annabi ﷺ 🤲💞

Anas Na Annabi
07018961555

• Head bloggers Department: Jamaatu media Kano state

28/09/2026

•AMADU GA HANNUNMU KARA ROKA MANA ALLAH🤲

•MAJALASIN YAU LITININ 28/9/2026🎤🎤 Insha Allahu Awannan Rana Ta Litinin Imamul Ahbabu Rasulilahiﷺ Maulana Sheikh Sharif ...
28/09/2026

•MAJALASIN YAU LITININ 28/9/2026🎤🎤

Insha Allahu Awannan Rana Ta Litinin Imamul Ahbabu Rasulilahiﷺ Maulana Sheikh Sharif Sani Janbulo Zai Gabatar Da Majalasi Na Fadar Girma Da Isa Da Matsayin ANNABIﷺ A Garin Dankwali, Wanda Yake A Yankin Karamar Hukumar Gezawa Jihar Kano.

Lokaci: Da Misalin Karfe 9:00 Na Dare Zuwa Abinda Yasauwaka Insha Allahu, Allah Yabada Ikon Zuwa Amin Summa Amin.

Address

Janbulo First Gate, Sharif Sani Street
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama'atu Media Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share