Tabarau Mag

Tabarau Mag Kawo muku Labarai da Rahotanni kan halinda Duniya ke ciki shine burin mu a ko da yaushe, ku zam bi-b

Tabarau Media kafar sadarwa ce da masu sha awa da shauki a bangaren yada labarai s**ayi hadaka wajen samarda ita.

15/08/2021

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun kamo duk waɗanda ke da hannu a kasar matafiya da matsasa ɗauke da mak**ai s**a yi Jos, Jihar Filato. Kakakin fadar shugaban kasa, Garba shehu ya fitar da wannan sanarwa da ya ke kunshe da sakon shugaban kasa. Sanarwar ta cigab...

Mai Sunan Shugaba Buhari Ya Koma Bakin Aiki Bayan Gane Cewa Ba Shida Wata Alaqa Da Karban Cin HanciDaga Comrd Zakariyah ...
13/08/2021

Mai Sunan Shugaba Buhari Ya Koma Bakin Aiki Bayan Gane Cewa Ba Shida Wata Alaqa Da Karban Cin Hanci

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe

Yanzu haka dai mutumin da'a kaita yada hotunan sa a kafafen sada zumunta na zamani bisa zargin karban cin hanci rashawa wanda batun ba shida tushe ballantana mak**a mai suna, Comrd Buhari Ishaq, wanda shine babban akawu a hukumar kula da mahajjata na jihar Gombe, ya kuma bakin aiki bayan da'aka gane cewa dukkanin abun da'ake zargin shi a kai bai aikataba.

A yanzu haka dai daruruwan mutane, marubuta, da Kuma gidajen jaridu daga sassa daban-daban na Arewacin kasar nan ke cigaba da neman yafiyan wannan bawan Allah sak**akon yada hotonansa da kuma yi masa batanci da s**a dinga yi ba tare da tabbatar da abun da ake zargin sa a kai ba.

Idan dai jama'a zasu iya tinawa, Malam Buhari shine wanda aka dinga yawo da hotonan sa sak**akon wani zargi da akace hukumar EFCC tana yi masa na karban cin hanci da rashawa, wanda kuma sam ba haka abun yake ba k**ar yadda Buharin ya bayyanawa Wakilin Jaridar Gaskiya Reporters cewa, aiki ne ya yiwa wani sai yaji dadi wanda sak**akon hakan ya yi mishi Ihsani, amma sam ba cin hanci ya karba ba.

Ba Cin Hanci Na Karba Ba, Aiki Nayi Aka Ji Dadi Sai Aka Min Ihsani ~ Muhammad BuhariDaga Comrd Zakariyah Salisu, GombeMu...
11/08/2021

Ba Cin Hanci Na Karba Ba, Aiki Nayi Aka Ji Dadi Sai Aka Min Ihsani ~ Muhammad Buhari

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe

Mutumin da ake ta yada hoton hotonsa a kafafen sadarwa na zamani bisa zargin yin awun gaba da wasu kudade mai sunan Shugaba Buhari ya fitar da sako na mussaman ga al'ummar jihar Gombe da ma Najeriya baki daya

Idan ba'a manta ba dai a makon da ya wucene a kaita yada hoton wani mai sunan Shugaba Muhammadu Buhari bisa zargin da hukumar yaki da cin hanci da rasha ta EFCC ke yi masa na yin awun gaba da wasu kudade, zargin da mutumin ya musanta.

Mutumin mai suna Comrd Muhammadu Buhari ishaq, wanda shine babban akawu hukumar ma'aikatan alhazai ta jihar Gombe. Ya rubuta budadiyar wasika zuwa ga al'ummar jihar Gombe dama kasa baki daya inda a cikinta ke karyata batun dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani kan cewa, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC na zarginsa da karban cin hanci da rashawa, lamarin da Buharin yace sam-sam ba haka batun yake ba.

Hakazalika ya kara da cewa shi dai abun da ya sani kan wannan batu shine maganar Kalmar da akayi amfanin da ita wajen tuhumar nasa , wato "Gratification" inda yace wannan kalmar kalmane ta Ihsani, kalmar na nufin k**ar ka yiwa mutum aikine yaji dadin aiki sai yayi maka wani abu na kyautatawa wanda kuma sam wannan abun babu ta yadda za'ayi ya zama cin hanci da rashawa k**ar yadda ya shaidawa duniya lokacin zantawarsa da wakilin gidan Rediyon Jewel FM a jihar ta Gombe.

Daga karshe Comrd Buhari ya ce kuma duk wanda s**aita yada wannan hoto ba tare da wani kwakwaran dalili ba, to su sani tabbas za su tashi ranar lahira su bada shaida a gaban Allah. Sannan Kuma ya kara da cewa, idan ma sun yine saboda cinma wata manufa, to babu makawa bayan cinma manufar tasu za suyi da dana sani.

wani batu dake yawo a shafikan sada zumun ta na yanar gizo da cewar hukumar EFCC ta k**asa bisa zargin da ake na cewar hukumar ta k**asa da kar6ar cin hanci a ma'aikatan hukumar alhazan. Wanda Kuma shi com. Buhari wannan batu bahaka yake ba, illah dai kawai abunda yasani wani abune da ake Kira "gratification" Wanda acewar sa wannan kalmar fassaran ta shine k**an k**awa mutun aiki ne yaji Dadi ya maka ihisani. Adan haka wannan ba cin hanci bane

04/08/2021

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Sokoto Ali Inname ya bayyana cewa an gano wasu ɗalibai ƴan bautar ƙasa 14 sun kamu da korona a jihar. Inname ya ce an gano wadannan ɗalibai ne sansanin horas da ɗaliban masu yi wa ƙasa hidima dake jihar. Ya ce tuni har an killace su gudun kada su sauran […]

04/08/2021

Mafarauta da maharban da su ka fantsama daji domin ceto ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri a Jihar Kebbi, sun ce sun daina neman yaran haka nan, domin gwamnatin jihar ba ta nuna masu cewa lallai da gaske ta ke yi, ta na so a sako yaran ba.. An dai k**a ɗaliban su 102 tun […]

03/08/2021

Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 kuma sun babbake gidaje 250 a masarautar Miango dake karamar hukumar Bassa jihar Filato. Ƴan bindigan sun kai wa masarautar hari ne a daren Asabar. Sakataren yaɗa labaran kungiyar Iregwe Davidson Malison ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Jos. Malison ya ce mahara...

EL-ZAKZAKY: Zamu daukaka kara – Gwamnatin Kaduna
31/07/2021

EL-ZAKZAKY: Zamu daukaka kara – Gwamnatin Kaduna

Lauyan dake ke wakiltar gwamnatin Kaduna a shari’ar El-Zakzaky ya Dari Bayero ya ce kotu a Kaduna va ta yi wa gwamnatin Jamus har adalci ba. Bayero ya ce maishari’a Kurada bai duba ainihin korafin da gwamnatin Kaduna ta mika a gaban kotu ba, saboda haka tabbas za mu daukaka kara, ko tantama babu...

Zamfara State University Admission List 2020/2021
31/07/2021

Zamfara State University Admission List 2020/2021

Zamfara State University, Talata-Mafara (ZAMSUT) admission list of candidates admitted into the university first-degree programmes for the 2020/2021 academic session. This s to inform all the candidates that applied for admission into the Zamfara State University, Talata-Mafara (ZAMSUT) first-degree...

Abu-ubaida Muhammad Mai Manhajar DayChat Ya Samu Ganawa Da kwamishinan Bunƙasa Harkokin Matasa Na Jihar Gombe.Daga Comrd...
14/07/2021

Abu-ubaida Muhammad Mai Manhajar DayChat Ya Samu Ganawa Da kwamishinan Bunƙasa Harkokin Matasa Na Jihar Gombe.

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe.

Matashin nan daya kirkiri manhaja Kwatankwacin WhatsApp mai suna DayChat, ya samu haɗuwa da g*i girma Kwamishinan bunkasa harkokin matasa na jihar Gombe Alh Abubakar Aminu Musa Talban Herwagana a ofishinsa a ranar laraba.

A zantawarsa da mai girma kwamishinan, Abu-ubaida ya shaida masa irin alfanu da kuma cigaban da Manhajar zata kawo jihar Gombe dama kasa baki daya, yace idan gwamnati da masu hannu da shuni s**a shigo to zai taimaka wajen samarwa matasa aikin yi dama samarwa gwamnati kudaden shiga.

Abu-ubaida ya kara da cewa idan ya samu amincewar gwamnati zai bude wajen horas da Matasa Fasahar Zamani ta yadda zasu dogara da kansu ba tare da jiran sai gwamnati ta basu aikin yi ba, haka kuma zai yi rijista da gwamnati da sauran hukumomi.

A nasa Bangaren mai girma kwamishinan ya yabawa Abu-ubaida a bisa namijin kokari da yakeyi don kawo cigaba, inda yace tabbas gwamnati zata taimaka masa kwarai da gaske, kuma shima a nasa bangaren zai taimaka da kuma shigar da kungiyoyi masu zaman kansu ciki domin suma su taimaka masa.

Ya kuma ce Abu-ubaida yayi namijin kokari wajen samar da Radio na yanar Gizo na Farko a shiyar Arewa maso gabashin Najeria dake yada shirye shirye a Harshen Hausa, ya kuma shawarce shi daya cigaba da kawo cigaba domin kuwa gwamnati na tare dashi a koda yaushe.

Daga karshe yakirayi yan siyasa, yan kasuwa da ma Al’umma dasu taimaka masa domin karfafa masa gwiwa.

DayChat Manhaja ce da zata baku dama domin ku sada zumunci kuma nan bada jimawa ba za’a saketa.

Akwai tattaunawa ta musamman da kwamishinan zaiyi da Zamani Radio ta yanar gizo wanda itama Abu-ubaida ya kirkireta da misalin karfe 10 zuwa 11 na hantsi na gobe Alhamis 15 ga watan Yuli.

Wadda za'a iya shiga daga ɗaya daga cikin wadannan madannai.

https://­onlineradiobox.com/­ng/zamani/

https://­mytuner-radio.com/­radio/­hausaxpress24-radio-4­78055/

https://oiradio.co/­zamani-radio-s272124

https://­www.listenonlineradio­.com/nigeria/­zamani-radio

https://raddio.net/­373983-zamani-radio/

Zuwa Ga Gomnatin Jihar Gombe Kan Alkawarin Da S**a Yi Na Tallafawa Al'ummaDaga Comrd Zakariyah Salisu, GombeYa k**ata Go...
14/07/2021

Zuwa Ga Gomnatin Jihar Gombe Kan Alkawarin Da S**a Yi Na Tallafawa Al'umma

Daga Comrd Zakariyah Salisu, Gombe

Ya k**ata Gomnatin jihar Gombe ta yiwa mutane bayani dangane da alkawarin da ta yiwa talakawa na tallafa musu da jari domin rage radadi karkashin Bankin Bubayero Microfinance Bank, wanda Kuma har yanzu jama'a sunji shiru babu wani Karin bayani.

Yana da kyau ace an fito domin sanar da jama'a saboda kowa da kowa cikin wanda s**a cike form din su san makomarsu. Kar ya zamana sunata yin jiran gawar shanu. Su sake baki kan alkawarin da gomnati ba zata iya cikawa. Saboda haka Gwamna Muhammy Inuwa Yahaya wannan kalu bale a kanka.

Wannan dai tinatarwa muke yiwa gomnatin jihar Gombe domin ta samu ta cika alkawarin data yiwa talakawan jihar Gombe.

© Zakariyah Salisu ✍️
Mai Kishin Jihar Gombe, Kano, Arewa Da Najeriya

Mutanen garin Kajuru sun ɗunguma fadar maimartaba sarkin Kajuru Alhassan Adamu domin nuna farin ciki da murnar sako sa d...
12/07/2021

Mutanen garin Kajuru sun ɗunguma fadar maimartaba sarkin Kajuru Alhassan Adamu domin nuna farin ciki da murnar sako sa da ƴan bidiga s**a yi. Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito daga bakin Madakin Kajuru wanda ɗan sarkin ne, ya ce suna zaune kawai sai s**a ga sarki ya shigo musu. ” Muna zaune ne fa kawai sai muka ji an yi mana sallama, ashe sarki ya dawo gida daga inda ƴan bindiga s**a tsare shi kuma shi kaɗai....

Mutanen garin Kajuru sun ɗunguma fadar maimartaba sarkin Kajuru Alhassan Adamu domin nuna farin ciki da murnar sako sa da ƴan bidiga s**a yi. Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito daga bakin Madakin Kajuru wanda ɗan sarkin ne, ya ce suna zaune kawai sai s**a ga sarki ya shigo musu. ” Muna zaune ne f...

Address

Kirfi, Bauchi
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tabarau Mag posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share