Hausavoice News

Hausavoice News Barka da zuwa wannan shafi namu mai albarka ka kasance damu awa 24 domin samun labarai nagaskiya

Wai mene dalilin kukan rakiya Musa?
12/04/2023

Wai mene dalilin kukan rakiya Musa?

Najeriya: Ba a biyan mu alawus — Masu tsaron iyakaJami'an tsaron da ke aiki na musamman don kula da iyakokin Najeriya wa...
30/03/2023

Najeriya: Ba a biyan mu alawus — Masu tsaron iyaka

Jami'an tsaron da ke aiki na musamman don kula da iyakokin Najeriya wajen hana satar shigar da haramtattun kaya, sun koka a kan rashin biyan su kuɗaɗen alawus-alawus na aiki.

Ma’aikatan sun koka ne tare da yin kira ga waɗanda lamarin ya shafa a kan su taimaka a biya su haƙƙoƙinsu.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da BBC ta tattauna da shi amma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, suna wahala ƙwarai da gaske a aikin.

Jami'in ya ce, ma’aikatan da ke aiki a tsare iyakokin Najeriyar don sanya idanu da hana shigar da haramtattun kaya da mutane ba bisa ƙa'ida ba, sun haɗar da sojoji da jami’an hukumar hana fasa-ƙwauri da jami'an shige da fice da kuma na hukumar ‘yan sandan farin kaya wato DSS.

A abuja Nigeria
27/03/2023

A abuja Nigeria

Mene ne hukuncina idan na kusanci matata cikin Ramadana da rana?Ibadar azumi tana buƙatar mutum ya ƙauracewa cin abinci ...
27/03/2023

Mene ne hukuncina idan na kusanci matata cikin Ramadana da rana?
Ibadar azumi tana buƙatar mutum ya ƙauracewa cin abinci da sha da kuma kusantar iyali daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.

Manufar ita ce jiki ya samu wani sauyi wanda bai saba ji ba, domin haka ne Ubangiji ya ce shi da kansa ke biyan lada ga mai azumi.

Sai dai a kan fuskanci matsaloli da dama a yayin azumin musammam ga sabbin aure ko kuma mutanen da suke ɓata-gari, wani lokacin kuma tsautsayi ya gifta ko da a kan waɗanda s**a shafe shekaru ne da aure, a samu kuskure ta fuskar mu'amalar iyali.

Mene ne hukuncin wanda ya kusanci iyalinsa cikin azumi?

CBN ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗiBabban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffi...
29/01/2023

CBN ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi

Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin kuɗi, saura kuma naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsofaffin kuɗaɗe.

Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwanaki 10.

RABA GARDAMA: ZAN DAWO LABARINA ACEWA NUHU ABDULLAHI.Fitaccen jaruminan mai suna nuhu abdullahi ya bayyanawa Fulani ng H...
28/01/2023

RABA GARDAMA: ZAN DAWO LABARINA ACEWA NUHU ABDULLAHI.

Fitaccen jaruminan mai suna nuhu abdullahi ya bayyanawa Fulani ng Hausa cewa zai dawo shirin labarina akowane irin lokaci.

Sakamakon yadda labarin ya sami sauyawa akan yadda aka faroshi.

Nuhu abdullahi ya kara da cewa yanawa dukkanin masoyansa godiya da fatan alkhairi.
Kannywood Legend Gallery

ATIKU YAROKI CBN DATA KARA WA,ADIN KARBAR TSAFFIN KUDADE.Dan takarar shugabancin kasar na jam,iyyar PDP wato atiku Abuba...
28/01/2023

ATIKU YAROKI CBN DATA KARA WA,ADIN KARBAR TSAFFIN KUDADE.

Dan takarar shugabancin kasar na jam,iyyar PDP wato atiku Abubakar ya bukaci CBN da ta kara wa,adin karbar tsofaffin kudade hakan ya biyo bayan zantawa da yayi da shugaban Babban bankin.

Inda ya roki da a sassautawa talakawa domin su sami sauki.

Atiku Abubakar

Wata sabuwa: gwamnatin kano ta dage taron da ta shiryawa shugaban kasa na kaddamar da wani aiki ranar litinin dinnan mai...
28/01/2023

Wata sabuwa: gwamnatin kano ta dage taron da ta shiryawa shugaban kasa na kaddamar da wani aiki ranar litinin dinnan mai zuwa.

Hakan yasa shakku a zuciyoyin alumma gameda dage zuwan nashi inda wasu ke ganin hakan ya biyo bayan abinda yafaru a katsina kokuma kawai wata tsatsamar alaka dake tsakanin gwamnatin jihar kanan da ta tarayya.

Amma menene ra,a yinku
Fulani ng Hausa

https://chat.whatsapp.com/CP5gFOf7JQ82AsBTAK68ou

GWAMNATIN JIHAR KANO TA ROKI GWAMNATIN TARAYYA DA TA KARA WA,ADIN KARBAR TSAFFIN KUDADE.Gwamnan jihar kano DR Abdullahi ...
28/01/2023

GWAMNATIN JIHAR KANO TA ROKI GWAMNATIN TARAYYA DA TA KARA WA,ADIN KARBAR TSAFFIN KUDADE.

Gwamnan jihar kano DR Abdullahi umar ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara wa,adin karbar tsaffin kudade duba da irin halin da jama,a suke ciki.

Jawabin yafito ne daga bakin komushinan kananan hukumoni murtala sule garo.

Inda ya gudanar da jawabin Nasa a jiya juma,a agidan gwamnatin dake kano.

Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗiKwanaki kalilan ne dai s**a rage a daina ...
28/01/2023

Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi

Kwanaki kalilan ne dai s**a rage a daina amfani da tsoffin takardun kuɗi a Najeriya kamar yadda Babban Bankin kasar ya sanar.

Babban bankin Najeriyar ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa'adin da ya sanya na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu.

Sai dai, bangarori da dama a cikin ƙasar na kira ga Babban Bankin da ya tsawaita wa'adin.

Ƴan Najeriya da dama na ƙorafi game da ƙarancin sabbin takardun kuɗin, inda s**a ce har yanzu bankunan ƙasar na bai wa kwastomominsu tsoffin takardun kuɗi.

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba ne Babban Bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar na naira 200 da 500 da kuma 1000, inda ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Lokacin kaddamar da sabbin kuɗin, shugaba Buhari ya ce sauya fasalin kuɗaɗen zai yi tasiri ƙwarai wajen taimaka wa ƙasar ta magance matsalar yaɗuwar kuɗi ba bisa ƙai’da ba da cin hanci.
Shugaban ya ce sabbin kudaden za su inganta tatalin arzikin Najeriya da ƙara wa kuɗin ƙasar daraja.

Mutane da dama na ta bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sada zumunta. Ga wasu da muka tsakuro muku daga shafukanmu.

Yellow Man ya ce: An bar karɓar tsoffin takardun kuɗi a yankinsu sannan masu shaguna ma sun rufe.

Address

NO:104 ALUAVENUE NASARAWA GRA KANO
Kano
700101

Telephone

+2347063374810

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausavoice News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausavoice News:

Share