20/08/2025
IN TAKALMI YAYI MAKA YAWA BA ZAKA IYA SAURI BA:
A rayuwa kowa da rabon da Allah ya tsaga Masa, kuma ba Mai iya samun fiye da qaddarar sa
Gaskiyar masu cewa: in kunnen ya wuce Kai mutum baya kyan gani, don haka Muna tsayawa iya matsayin mu don mu hutar da zukatan mu
Ba Mai azabtar da kansa a rayuwa irin Wanda ya dorawa Kan sa kayan da banzai iya Kai su gaci ba
Ina amfani wadannan abubuwa a rayuwa???
1. Karantar da littafi da ya wuce ilimin ka
2. Hidimar kudin da ta wuce samun ka
2. Rike matar da ta wuce dukiyar ka
3. Zama a gidan haya da ya wuce samun ka
4. Saka tufafin da s**a fi arzkiin ka
5. Adawa da Wanda ya fika tsoron Allah
6. Tozarta Wanda ya fika kirki da mutumci
7. Fada da hukuma, ko bijirewa shugaba
8. Hassada ga Wanda yake samu daga Allah
9. Nuna kauna da damuwa ga Wanda baya son ka
Allah ya tsare mana mutumcin mu da Imanin mu, amin