Double Spy Media solutions

Double Spy Media solutions Double Spy Media solutions was a small agency with big dreams and talent to make those dreams realit

25/09/2024

Alhamdulillahi masha Allah a duba comment section

21/12/2023

وأما من خاف مقام ربه ونهى النفس عن الهوى...

Pls follow us, like & share👇
17/10/2021

Pls follow us, like & share👇

1 Followers, 5 Following, 0 Likes - Watch awesome short videos created by DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

27/09/2021

ALBISHIR A GAREKI GANGARIYA
Cibiyar bincike da wayar da kan mata, tare da inganta lafiyar aure da zamantakewa ta DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

Ta fara siyar da form tare da yin rijistar mata na seminar taron da ta saba gabatarwa a Mambayya mai taken:
"YADDA AKE RAYUWA DA ABUBUWAN DA AKE RAYUWA TARE DA SU A GIDAN AURE" (ido-da-ido).
yi kokarin yin rijistar kafin adadin da aka diba ya cika, don adadin matan da ake bukata a kididdige suke.

GARAƁASA DA SABON SALO CIKIN TSARI:
Zamu koyar da abubuwa 3 cikin tsari3 kyauta..

A- ZAMU KOYAR DA MATA YADDA AKE HADA TURARUKA;
1. Arabian perfumes (masu kara kauna da shauki a tsakanin ma'aurata)
2. Humrah (Mai zaqi da mai taushi da mai kamshi)
3. Na garwashi (domin gyara bututu dana ije fitina)

B- ZAMU KOYAR DA MATA YADDA AKE WASU GIRKE-GIRKE NA MUSAMMAN;
1. Na gargajiya (mai ma'ana)
2. Na Zamani (mai amfani)
3. Na Dake Ake (mai karawa mace daraja)

C- YADDA AKE KASHE WUTAR FITINA A RAYUWAR MA'AURATA;
1. A farkon aure (idan an kasa gina fahimta da kauna)

2. A tsakiyar aure (idan soyayya ta fara sanyi, ko shaidan yayi matsuguni)

3. Yayin karba da bayarwa (idan sugar yayi kadan ko gishiri yayi yawa)

AKWAI MISALAI DA BATUTUWA MASU DIMBIN YAWA A TARON BANA

Ga wadanda ba zasu iya halartar taron ba saboda wasu dalilai, ko wadanda ba mazauna Kano ba, zasu iya biya ta bank, bayan taro a aike musu da package en har inda suke

KUDIN YIN RIJISTA DA NA FOM: ₦2,050 (dubu biyu da naira hamsin kacal👌🏻)

ANA IYA YIN RIJISTAR K**AR HAKA;
Ofishin mu: Shop No 4 Plot 275 Ja'oji Quarters, Torrey Home Line, opp Zoological Garden (Exit-Gate), Zoo Road, Kano State, Nigeria.

Ko, ta banki akan:
Fidelity Bank
6312616639
Hadiza Balanti
Savings
🌹 🌹 🌹
Hadiza Balanti
Founder | CEO
DAKE AKE Global Consultancy
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
GA MASU NEMAN KARIN BAYANI A DANNA LINK DIN DAKE KASA:👇🏻
https://wa.me/message/RG75JQQCL5YTN1

Ko a kira:
081 2222 8484,
080 3953 4188,
080 3888 9681,
070 26 111 777
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
A TAYA MU DORA FLYERS EN A DP DA STATUS, SANNAN A YADA MANA WANNAN RUBUTUN A GROUPS DA SOCIAL MEDIA GABADAYA

The Double Spy Media Solutions team is comprised of veteran media personnel from production management, purchasing, esti...
02/11/2020

The Double Spy Media Solutions team is comprised of veteran media personnel from production management, purchasing, estimating and sales.

Cumulatively, our experience surpasses 100 years of providing media solutions for clients ranging from small, entrepreneurial start-up companies to marketing agencies to Fortune 100 clients.

SANARWA DA BABBAN MURYA DAGA RUNDINAR SOJIN NIGERIA Rundinar sojin Nigeria ta shirya wani gagarumin rawar daji da atisay...
18/10/2020

SANARWA DA BABBAN MURYA DAGA RUNDINAR SOJIN NIGERIA

Rundinar sojin Nigeria ta shirya wani gagarumin rawar daji da atisaye mai taken MURMUSHIN-KADA karo na hudu (CROCODILE SMILE VI) wanda zai gudana a fadin Kasar Nigeria gabaki daya

Wannan gagarumin rawar daji mai k**a da ruwan dare gama duniya rundinar sojin Nigeria zata fara gudanar da shi ne nan da kwanaki biyu masu zuwa, wato jibi Talata 20-10-2020, zata kammala zuwa ranar Alhamis 31-12-2020

Rawar dajin zai kalubalanci ta'addancin Boko Haram musamman 'yan Boko Haram da suke gudowa daga dazuka zuwa wasu yankuna na Nigeria da kuma 'yan bindiga da s**a buya a daji, sannan za'a kalubalanci masu yada kalaman karya da farfaganda wanda ya shafi tsaron kasa a kafofin sada zumunta na zamani

Sannan rawar dajin zai kalubalanci duk wata matsala dake da barazana da tsaron Nigeria gabaki daya, don haka rundinar sojin Nigeria tana tabbatarwa mutanen Nigeria masu son zaman lafiya cewa wannan rawar dajin ba zai taba su ba, kuma rundinar na neman goyon bayansu, k**ar yadda sanarwa ya fito daga mukaddashin kakakin rundinar sojin Nigeria Kanar Sagir Musa

Jama'a wannan rawar dajin yazo a kan gaba, domin Nigeria tana fuskantar barazana tsaro game da masu gudanar da zanga-zangar ENDSARS wanda yake neman rikidewa zuwa wani abu dabam dake tattare da barazana wa tsaron Nigeria, ni a fahimtata wannan rawar dajin yana da nasaba da kalubalantar mummunan shirin da makiya zaman lafiyar Nigeria ke yiwa Kasar

Jama'a kun tuna lokacin da tsageru masu rajin kafa Kasar Biafra s**a dauki makami karkashin jagorancin tsageri Nnamdi Kanu zasu kafa Kasar su? a daidai lokacin ne rundinar sojin Nigeria ta kaddamar da rawar daji mai taken MURMUSHIN KADA karo na farko wanda ya tilasta guduwar Nnamdi Kanu daga Nigeria

Don haka yanzu ma da s**a kawo ENDSARS sai rundinar sojin Nigeria ta sake kawo MURNUSHIN KADA, kuma tuni babban makiyin zaman lafiyar Nigeria shedani Femi Fani Kayode har ya fito ya yiwa rundinar sojin Nigeria da gwamnatin Buhari raddi akan wannan yunkuri na murmushin kada da rundinar sojin Nigeria zata fara

Wallahi na jima banji dadi akan wani matakin tsaro da rundinar sojin Nigeria ta dauka akan lokaci ba k**ar wannan, hankalina ya fara kwantawa, dama masu karin magana s**ace: "maganin biri mai wayo sai karen maguzawa"

Allah Ka taimaki rundinar sojin Nigeria
Allah Ka haramta makiya zaman lafiyar Nigeria samun nasara
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum🙏

HALAYYAR MAFI YAWAN 'YAN AREWA YAYI K**A DA NA KIFI "GAIWA"Wannan itace GAIWA, wata halitta ce dake rayuwa a cikin ruwa ...
16/10/2020

HALAYYAR MAFI YAWAN 'YAN AREWA YAYI K**A DA NA KIFI "GAIWA"

Wannan itace GAIWA, wata halitta ce dake rayuwa a cikin ruwa ta fito daga jinsin kifi, tana k**a da TARWADA a siffa, amma halayyarta daban take da ta tarwada.

A zahiri za'a ga k**ar tana da hakuri da rashin son fitina, sai dai takan kasance cikin damuwa da tashin hankali a duk lokacin da taga wata 'yar uwarta GAIWA na neman yin abin kirki.

GAIWOWI s**an taru su cinye duk GAIWAR da s**aga alamun daukaka ta bayyana gareta, duk da cewa GAIWA tana haifar 'ya'ya masu yawa, sai dai bata da abincin da ya wuce 'ya'yanta ko 'ya'yan wata Gaiwar wanda hakan ya sa rayuwar GAIWA take kasancewa kuntacecciya.

A wajen Gaiwa da 'yar uwarta taci gaba har tayi girma, gwara 'ya'yan Tarwada su girma, ita nata ne kawai bataso.

Sanin halayyar GAIWA hakan yasa Malam Aminu Kano ya dade yana kiran mutanen Arewa musammam talakawa akan su gujewa kwaikwayon rayuwar GAIWA.

Amma da dukkan alamu, a yanzu mun kwarance a kalar rayuwar GAIWA, da wahala kaga namu yana kaunar namu, burinmu namu ya karye don kawai bamu bane, gani muke k**ar gwara kowa da namu .

Allah Ka shiryemu Ka bamu kaunar juna, ka tsaremu daga halin gaiwa. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

GWAMNATIN NIGERIA TA HARAMTA ZANGA-ZANGABayan karban shawarwari daga masana tsaro da masu iko da tsaron Kasa s**a isarwa...
15/10/2020

GWAMNATIN NIGERIA TA HARAMTA ZANGA-ZANGA

Bayan karban shawarwari daga masana tsaro da masu iko da tsaron Kasa s**a isarwa shugaba Buhari, gwamnatin Nigeria ta haramta cigaba da gudanar da zanga-zangar ENDSARS a fadin kasar Nigeria gabaki daya

Dokar haramcin ya fara aiki daga yau Alhamis, Gwamnati ta bawa jami'an tsaro umarni da su dauki matakin kamewa da tarwatsa duk wata rundina ta masu gudanar da zanga-zangar ENDSARS

Masu zanga-zangar ENDSARS an yi musu abinda suke so amma sunki denawa, iskancin nasu yana neman wuce iyaka, umarnin da aka bawa jami'an tsaro su tarwatsasu yayi daidai

Yaa Allah Ka mana maganin duk wani tsageri da mai mugun nufi akan zaman lafiya da tsaron Kasarmu Nigeria Amin

DATTI DATTI

15/10/2020

Idan kana bibiyar zanga-zangar zaka fahimci cewa sunada wata boyyayar manufa.

A yanzu danake wannan rubutun sunada kusan Naira miliyan 50 ta suke tarawa a tsakanin su, don siyan abinci, kuma har har yanzu basu daina karbar tallafi ba.

Acikin daren jiya CEO din Twitter yayi verifying accounts wadanda suke kan gaba a zanga-zangar yakuma bude musu sabowar hanyar da zasu karbi taimako ta hanyar bitcoin.

Ba ina kokarin kashewa masu shirin zanga-zanga a arewa gwiwa bane, amma ina ganin yak**ata muyi tunanin abubuwa k**ar haka.

1. Idan tunanin yan kudu shine kawo juyin juya hali a Nigeria, yin zanga-zanga a arewa bazai taimakawa kudrinsu ba?

2. Munsani hukumar yan sanda tana karkashin ikon gwamnati, hakan na nufin gwamnati zata iya sawa ko hanawa, haka kan boko haram da yan ta'adda? Idan ba haka bane, muna tunanin zanga-zanga ce, zatayi aiki?

Idan dan kudu yace gwamnati ta dau biro da soke SARS, hakane da banditry da kuma Boko Haram?

Tabbas idan borin yan kudu shine kawo juyin juya hali, to zanga-zangar yan arewa zata kara rikita Nigeria kawai, kuma hakan taimakon su.

-ISMA'IL AUWAL

ABINDA YAKE FARUWA A WANI YANKI NA ABUJAHar zuwa yanzu tsageru makiya zaman lafiyar Nigeria sun cigaba da gudanar da zan...
15/10/2020

ABINDA YAKE FARUWA A WANI YANKI NA ABUJA

Har zuwa yanzu tsageru makiya zaman lafiyar Nigeria sun cigaba da gudanar da zanga-zangar ENDSARS duk da dokar haramci musamman a babban birnin tarayya Abuja, abin nasu ya rike zuwa juyin juya hali

Yanzu a haka a yankin Gwarinfa cikin Abuja sun tare motoci bila'adadin, ga tsananin ruwan sama da yake sauka, kuma sun hana a wuce, idan sunga mota mai tsada sai su buga su bukaci a basu kudi ko su fasa gilashi

Abinda yake faruwa kenan a garin da masu iko da kasar suke, kuma babu wani jami'in tsaro da aka tura gurin b***e ma a hanasu, haka a cikkn ruwa ake bin masu zanga-zangar ana basu abinci da ruwan sha, a kan t**i zasu kwana, ku tambayi kanku jama'a waye yake daukar nauyin ciyar da masu zanga-zangar?

Yau inda Hausawa ne mutanen Arewa s**ayi abinda yake faruwa yanzu haka a Abuja da an bude musu wuta an kashe, da yanzu ana lissafin gawarwakin da aka kashe, amma wadannan da yake masu uwa a gindin murhu ne zasu aikata abinda s**a ga dama babu uban da ya isa ya tabasu

Asalima na ga mukarraban shugaba Buhari suna ta rarrashin masu zanga-zangar ENDSARS din, sannan ana ta fitar da sanarwan gargadi ga jami'an tsaro da kada su far musu saboda shafaffu da mai ne

Ba shakka mutanen nan sunfi karfin gwamnatin Buhari da mukarrabansa, mafita kawai Buhari yayi kokarin sasantawa da kungiyar ASUU su janye yajin aiki dalibai su koma makaranta, hakan zai rage dandazon masu zanga-zangar tun da sunfi karfin a dakatar da su

Allah Ya kawo mafita na alheri

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Double Spy Media solutions posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share