25/10/2024
๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐
Assalamu alaikum
Yau DCTV Africa ta cika Shekara guda zama registered Academy, sannan tsawon shekara 3 kenan muna koyarwa tun daga lokacin Arbitrage trading wato karta kati ๐
Tsawon wannan lokaci mun yaye dalibai masu yawan gaske, amma har yanzu bamu samu yanda nake so ba, wato naga dalibai na sun tsaya da kafarsu.
Bayan Bincike na gano cewa mafi yawan sun koya sun kware, amma basu da jarin da zasu dinga shiga kasuwa dashi domin amfanar abinda s**a koya har su yiwa kansu rana.
Wannan dalilin yasa muka fito da tsarin "DCTV Africa Trading SQUAD"
A wannan tsarin zamu duba dalibanmu jajirtattu mu saka su a wuri daya mu basu karin horo na musamman sannan mu basu jari da zasu dinga s**a kasuwa dashi, a hankali su dawo da kudin sannan a dinga raba riba. Na ware Dala Dubu daya ($1,000) daga aljihuna domin farawa da studens 20, ($50 each)
Yanda abinda zai kasance:
1. Zamu duba students daga s**a fi kowa jajircewa wurin "Practice" a cikin group namu na Tele..gram na DCTv Africa.
2. Zamu basu karin horo na musamman yanda ake shiga kasuwa da strategies na scalping.
3. Zamu zuba Dala hamsin ($50) a cikin exchanges mallakarmu sai mu baiwa students 20 log in details, suyi log in su dinga trading da wannan kudin. Kasancewar details na wannan account din yana wurinmu, mutum bazai iya withdrawal ba, sai dai yayi trading kawai.
4. A lokacin da students ya samu trading da yakai 50%, ma'ana kudin s**a kai ($75), toh zamu dinga cire masa 70% na duka profit da yayi making, sauran kuma a dinga barshi a account din.
5. Idan kudin s**a kai ($100) zamu cire ($50) mu baiwa wani ma, shi kuma wannan account din a dinga raba ribar da aka samu 70:30, wato Student ya dauki 70%, DCTV Africa ta dauki 30%. har zuwa lokacin da student ya yanke shawarar zai daina wannan alakar sai mu bar masa kudin da suke account din yaje ya cigaba da rayuwarsa.
6. Idan student yayi asarar sama da 50% na account din, ma'ana kudin s**a ragu zuwa $25 toh zamu karbi account din mu baiwa wani, ya koma ya kara karatu bayan wani lokaci mu kara bashi dama.
In sha Allah zamu fara wannan program immediately, ma'ana daga yau 25th October, 2024 zamu dauki students da s**a cancanta mu fara musu karatu na tsawon sati biyu. Ranar 10th November, 2024 zamu bayar da wannan accounts garesu in sha Allah.
Muna fatan Allah ya sanya mana albarka a wannan program ace daga yanzu zuwa shekara mai zuwa ace wannan kudi sun koma kamar $50,000, sannan ace munyi empowering kamar matasa 1,000 ko fiye da haka.
In sha Allah daga cikin wannan riba da zamu dinga samu zamu dinga wasu ayyukan kamar ciyarwa, scholarships na karatu a skills daban daban da sauransu.
Ku saka mu addu'o'inku Allah ya mana jagora.
Muna maraba da shawarwari da gudunmawa ta kowanne fanni. Amma fa ba bara muke ba domin in sha Allah mun fi karfin muje bara ko'ina a duniya. Kawai mun bude kofar ne ga masu sha'awar shiga aikin alkhairin.
Sannan kar kaga nace na ware kudi zan yi empowring students ka min dm cewa na taimake ka ko na taimakeki, bazan yi ba gaskiya, ni gina al'umma nake na kashe musu zuciya ba.
Muna fatan duk wani lada da zamu samu a wannan aiki, Allah ya kaiwa mai gidanmu da ya nuna mana wannan hanyar Sheikh Muhammad Auwal Albaniy Zaria kabarinsa. Allah ya jaddada Rahama a gareshi. Da sauran shehunan crypto da s**a taimaka mana har muka zama abinda muke a yau kamar Mahmoud Muh'd Sardauna Sunusi Danjuma Ali Engr Usman Bello Abdullahi da sauransu